“Muna Samun Nasara a Yaki da Ƴan Ta’adda a Arewa Maso Yamma,” in Ji Rundunar Soji
- Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta na ci gaba da nuna kwazo da sadaukar da kai a yaki da 'yan ta'adda da masu tayar da kayar baya
- Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai
- Nwachukwu ya ruwaito yadda dakarun suka yi nasarar kakkabe 'yan bindiga 12 tare da kwato babura guda 10 a samamen da suka kai Zamfara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kakkabe 'yan bindiga 12 tare da kwato babura guda 10 a yayin wani samame da suka kai jihar Zamfara.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya ce sojojin a ranar Litinin 15 ga Afrilu, 2024, sun lalata sansanin ‘yan ta’adda a karamar hukumar Maru ta jihar.
Nwachukwu ya ce sojojin da suka yi aiki da sahihan bayanan sirri sun kaddamar da harin domin tarwatsa sansanin da da kuma kashe 'yan bindigar da ke zama a wajen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kayayyakin da sojoji suka kwato
Ya kara da cewa sojoji sun kashe 12 daga cikin ‘yan ta’addan bayan wani kazamin artabu da wanda ya tilastawa wasu 'yan bindigar tserewa, jaridar Leadership ta ruwaito.
Sojojin sun kuma kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, gidan harsashi guda daya, alburusai masu tsayin 7.62mm (na musamman) guda 12, da kuma bindigu na gida guda biyu.
Sojojin sun kuma kwato babura guda 10 masu aiki da ‘yan ta’addan ke fita aiki da su tare da kwato shanu 18 da aka sace.
Nasarar sojoji kan 'yan bindiga
Jaridar The Cable ta ruwaito Nwachukwu na cewa:
“Sakamakon nasarar da aka samu ya nuna kwazo da sadaukarwar da sojojinmu suke yi wajen yaki da ta’addanci da masu tayar da kayar baya.
“Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron ‘yan kasar kuma za ta ci gaba da daukar kwararan matakai na dakile ayyukan ‘yan ta’adda a yankin."
Daraktan hulda da jama’a na rundunar ya jaddada aniyar rundunar na ci gaba da yin nasara a kokarin da ake na kawar da 'yan ta'adda daga yankin Arewa maso Yamma da kasa baki daya.
Ganduje na fuskantar sabuwar tuhuma
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihat Kano, Abdullahi Umar Ganduje na fuskantar sabbin tuhume-tuhume daga hukumar yaki ra rashawa ta jihar.
Muhyi Magaji, shugaban hukumar ne ya bayyana hakan yana mai cewa sun gabatar da tuhume-tuhumen da suka hada da karkatar da kudin kananan hukumomi da sauran su.
Asali: Legit.ng