Sojojin Najeriya Sun Dira Sansanin Manyan Ƴan Bindiga 3 a Arewa, Sun Kashe da Yawa Ranar Sallah

Sojojin Najeriya Sun Dira Sansanin Manyan Ƴan Bindiga 3 a Arewa, Sun Kashe da Yawa Ranar Sallah

  • Dakarun sojojin saman Njeriya sun farmaki sansanonin manyan ƴan ta'adda a kananan hukumomi 3 na jihar Zamfara
  • Mai magana da yawun NAF, Edward Gabkwet ya ce luguden wutan da jirage suka yi, ya halaka ƴan bindiga masu yawa ranar Sallah
  • Sojojin sun kaddamar da wannan farmaki ne ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2024, ranar da al'ummar musulmi suka yi sallar idi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ta samu nasarar halaka ƴan bindiga masu ɗumbin yawa a yankunan kananan hukumomin jihar Zamfara ranar Sallah.

Ruwan wutar NAF ya yi ajalin ƴan bindiga masu yawa a sansanin kasurgumin ɗan bindigan nan, Abdullahi Nasanda, a ƙaramar hukumar Zurmi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke hatsabibin ɗan ta'adda da ya yi ajalin janar din soja da wasu sojoji 3

Sojojin sama.
Sojoji sun murƙushe yan bindiga da yawa a jihar Zamfara Hoto: Nigeria Air Force
Asali: Twitter

Haka nan kuma ƙarin luguden sojin ya kashe da yawa daga cikin ƴan bindiga a sasanin hatsabibin ɗan bindiga, Mallam Tukur a ƙaramar hukumar Gusau jiya Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar, Air Vice Marshall Edward Gabkwet, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da NAF ta wallafa a shafinta na manhajar X ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu.

Ya ce sojoji sun kai farmakin ta sama ne bayan tabbatar da bayanan sirri da aikin leken asiri (ISR).

Yadda sojoji suka kai samamen

"Bayan sun tabbatar da cewa ayyukan na su ya yi daidai da na ‘yan ta’adda, jiragen sojoji sun bi ta sama sun saki wuta , wanda ya yi sanadin kashe ƴan bindiga da dama.
"Haka nan an gudanar da aikin ISR a sansanin Mallam Tukur, nan ma aka gano ƴan bindigar, ruwan wuta ta sama ya halaka su da yawa kuma an ga rumfunan su duk sun ƙone"

Kara karanta wannan

InnalilLahi: Ƴan bindiga sun halaka jami'an tsaro 30 ana shirin ƙaramar sallah a Arewa

"Sojojin ba su tsaya nan ba sun kuma kai samame kauyen Kani Kawa a karamar hukumar Maradun, inda suka gano mafakar ƴan bindiga da kayan aikinsu, suka murƙushe su."

- Air Vice Marshall Edward Gabkwet.

An kama babban ɗan ta'adda

A wani rahoton na daban Rundunar sojoji a Najeriya ta sake yin nasara inda ta cafke kasurgumin dan ta'adda da ake nema ruwa a jallo a jihar Adamawa.

Dakarun sun cafke Saidu Hassan Yellow ne a kasuwar Mubi da ke jihar Adamawa a ranar 9 ga watan Afrilu na wannan shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel