Sojojin Najeriya Sun Hallaka ’Yan Ta’adda da Dama a Jihar Zamfara

Sojojin Najeriya Sun Hallaka ’Yan Ta’adda da Dama a Jihar Zamfara

  • Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama a karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara
  • Nasarar ta zo ne bayan kazamin artabu da aka yi tsakanin sojojin da 'yan ta'adda a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu
  • Rundunar sojin ta bayyana nasarar a matsayin alama ta jajircewar sojojin kuma ta tabbatar da cigaba da kai farmaki kan 'yan ta'addan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Sojojin Najeriya da aka tura domin yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso yamma sun hallaka 'yan ta'adda da dama a jihar Zamfara.

Artabun da ya jawo an samu nasarar a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bindige 'yan sakai da fararen hula yayin harin Filato? Gaskiya ta fito

Sojojin Najeriya
Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a maboyarsu a Zamfara. Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Bayan sojojin sun yi gagarumin kutse a cikin 'yan ta'addar a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara sun lalata sansaninsu tare da fatattakar da dama daga cikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin da sojojin suka kashe

Bayanan da rundunar sojin Najeriya ta bayyana a shafinta na Facebook ya nuna cewa sojojin sun yi kazamin artabu da ‘yan ta’addar.

Daga bisani sojojin su kashe 12 daga cikin ‘yan ta’addan yayin da sauran kuma suka ari ta kare.

Barnar da sojojin suka yi wa 'yan ta'adda

Sojojin sun kuma kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, bindigu na gida guda biyu da tarin harsashi.

Bugu da kari, sojojin sun kwato babura guda goma da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen zirga-zirga da kuma shanu 18 da suka sace.

Daga baya sojojin sun lalata sansanin 'yan ta'addar bayan sun fatattake su.

Kara karanta wannan

Luguden sojoji: Manyan ƴan ta'adda da mayaƙa sama da 30 sun baƙunci lahira a Arewa

Rundunar sojin Najeriya ta ce wannan nasarar da suka samu wata sheda ce ta sadaukarwar da sojojin suka yi wajen yakar ta'addanci.

Ta cigaba da cewa zasu cigaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da kuma daukar kwararan matakai na dakile ayyukan ‘yan ta’adda a yankin.

Sojoji sun ceto mutane a Zamfara

Haka zalika kun ji cewa akalla mutane bakwai da suka hada da jarirai biyu da mata biyar ne dakarun sojoji na rundunar Hadarin Daji suka kubutar a jihar Zamfara

Kakakin rundunar, Suleiman Omale ya ce watanni biyu wadanda aka kubutar suka shafe a hannun masu garkuwa da mutane a dajin

Asali: Legit.ng

Online view pixel