Ganduje: APC da PDP Sun Rikice, Shugabanninsu Sun Shiga Garari, an Gano Dalili

Ganduje: APC da PDP Sun Rikice, Shugabanninsu Sun Shiga Garari, an Gano Dalili

  • Shugabannin jam'iyyun PDP da APC a Najeriya sun shiga mawuyacin hali yayin da ake neman tumbuke su a kujerunsu
  • A jiya, jam'iyyar APC a mazabar Dr. Abdullahi Ganduje ta sanar da dakatar da shi kan zargin cin hanci da rashawa
  • Yayin da shugaban PDP, Umar Damagun ke fuskantar matsin lamba kan dole sai ya yi murabus daga mukaminsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Siyasa a Najeriya ta sauya salo yayin da manyan jam'iyyun kasar guda biyu ke fuskantar matsala.

Shugabannin jam'iyyar APC da PDP a lokaci guda sun fuskanci kalubale daga mambobinsu game da wasu zarge-zarge.

Yayin da Ganduje ke cikin matsala, shugaban PDP ya gamu da cikas
An taso shugabannin jam'iyyar APC da PDP a gaba yayin da aka dakatar da Ganduje. Hoto: Umar Damagun, Abdullahi Ganduje.
Asali: Facebook

Musabbabin dakatar da Ganduje a APC

Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya shiga wani yanayi bayan mambobin jam'iyyar a mazabarsa da ke jihar Kano sun dakatar da shi.

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi": Tsohon hadimin Buhari ya magantu kan dakatar da Ganduje daga APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ta ce ta dakatar da shi ne saboda zargin cin hanci da ake zarginsa a kai har sai an kammala bincike.

Daga bisani shugaban jam'iyyar a Kano, Abdullahi Abbas ya dauki mataki inda ya dakatar da wadanda suka yanke hukuncin a jihar.

Har ila yau, wadanda ake zargin sun dakatar da Ganduje sun musanta haka inda suka ce ba su da hannu a wannan lamarin.

Ana zargin cewa jam'iyyar NNPP ce ta dauki nauyin wadanda suka sanar da wannan yunkuri na ganin bayan shugaban APC na kasa.

Matsalar da PDP ke fuskanta

A bangare guda kuma, neman dakatar da shugaban jam'iyyar PDP, Umar Damagun ya kara tsami yayin da ake shirin gudanar da babban taron jam'iyyar.

Leadership ta tattaro cewa wasu daga Arewa ta Tsakiya ne ke neman Damagun wanda ya fito daga Arewa maso Gabas ya yi murabus daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Tuhumar rashawa: Jam'iyyar APC ta dauki mataki mai tsauri kan Abdullahi Ganduje

Bukatar murabus na Damagun ba ta rasa nasaba da takun saka da ke tsakanin Atiku Abubakar da Nyesom Wike.

Masu kiran murabus din Damagun suna zargin cewa ya na yi wa jam'iyyar APC aiki ne ta bayan fage, cewar rahoton Punch.

Irin wannan dakatarwa daga matakin unguwa shi ya yi sanadin kujerar tsohon shugaban APC, Adams Oshiomole da tsoffin shugabannin PDP, Uche Secondus da kuma Iyorchia Ayu.

An zargi NNPP kan dakatar da Ganduje

Kun ji cewa, wata kungiyar mai suna PFM ta bukaci cafke wadanda ke da hannu a dakatar da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje.

Kungiyar ta zargi Sanata Rabiu Kwankwaso da daukar nauyin wadanda suka dakatar da Ganduje a jami'yyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel