Bikin Sallah: ’Yan Sanda a Kano Sun Kama Mutum 54 Masu Yunkurin Hargitsa Hawan Sallah

Bikin Sallah: ’Yan Sanda a Kano Sun Kama Mutum 54 Masu Yunkurin Hargitsa Hawan Sallah

  • 'Yan daba sama da 50 ne dauke da miyagun kwayoyi da muggan makamai suka yi yunkurin tayar da tarzoma a lokacin hawan Sallah a jihar Kano
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da nasarar kama 'yan dabar
  • Ana san ran gudanar da hawan sallar ne da yammacin Asabar, 11 ga watan Afrilu, a fadar mai martaba sarkin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bankado makarkashiyar da wasu ‘yan bangar siyasa suka shirya don hargitsa bikin hawan daushe da za a gudanar a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Bayan kama 'yan dabar, jami’an tsaro a jihar sun kara tabbatar da cewa sun kammala dukkan tanadi domin tabbatar da gudanar da bikin cikin lumana.

Kano CP
Za'a gurfanar da wadanda ake zargin da zarar 'yan sanda sun kammala bincike a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa Asali: Facebook
Asali: Facebook

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook ya tabbatar da cewa an tura isassun ma’aikata zuwa wurare masu mahimmanci domin kare lafiyar al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a hukunta duk wani mai laifi

Rundunar ta bayyana cewa duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a jihar za a kama shi kuma zai fuskanci fushin hukuma.

A cewar hukumar, ba za a nuna bambanci tsakanin masu aikata laifin da masu daukar nauyinsu ba.

Hawan sallah ba siyasa ba ce

A yayin bikin, hukumar ta haramta amfani da duk wani abu da zai nuna alamun jam’iyyun siyasa kamar riguna, alluna da sauransu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon dan majalisar wakilai ya yanki jiki ya fadi bayan dawowa daga sallar idi a Abuja

Har ila yau, hukumar ta shawarci ‘yan siyasa da su dauki Sallah a matsayin bikin hadin kai ba bikin nuna adawa ba.

Sun kuma sanar da cewa ana sa ran gurfanar da mutum 54 da ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.

An bankado shirin rikita Kano

A wani rahoton kuma, kun ji cewa wasu kungiyoyin addinai da siyasa sun shirya wargaza bikin sallar kan shari’ar Sheikh Abduljabbar da masarautun Kano.

An samu bayanin ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Abdullahi Kiyawa ya fitar a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel