Abduljabbar: ’Yan Sanda Sun Bankado Shirin Kungiyoyin Addini da Siyasa Domin Rikita Kano

Abduljabbar: ’Yan Sanda Sun Bankado Shirin Kungiyoyin Addini da Siyasa Domin Rikita Kano

  • Yayin da ake shirin gudanar da bukukuwan sallah a Kano, rundunar ‘yan sanda ta bankado shirin kawo tsaiko a zaman lafiyar jihar
  • Rundunar ta ce wasu kungiyoyin addinai da siyasa sun shirya wargaza bikin sallar kan shari’ar Sheikh Abduljabbar da masarautun Kano
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Abdullahi Kiyawa ya fitar a yau Litinin 8 ga watan Afrilu a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano sun bankado wani shiri na kawo tsaiko a bukukuwan sallah da za a yi.

Rundunar ta tabbatar da cewa ta samu labarin wasu kungiyoyin addini da siyasa na shirin ta da zaune tsaye a jihar yayin bikin.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Daso, an sanar da mutuwar wata matashiyar jarumar fina-finai

'Yan sanda sun gano shirin birkita Kano yayin bikin sallah
Yn sanda sun gano shirin kungiyoyin addini da siyasa domin kawo cikas a bukukuwan sallah a Kano: Kano Police Command.
Asali: Twitter

Gargadin da 'yan sanda suka yi a Kano

Kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a yau Litinin 8 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel ya bayyana cewa rundunar ta shirya tabbatar da doka a fadin jihar.

Gumel ya ce suna saka ido kan masu daukar nauyin wannan shiri na ta da tarzoma inda ya shawarce su da su janye wannan kuduri nasu.

Wane shiri aka bankado a Kano?

“Muna sane da dukkan shirinsu kuma mun shirya daukar mummunan mataki kansu har sai dai idan sun sauya tunani.”
“Rundunarmu ta na sane da shirin wasu kungiyoyin siyasa da addini da suka matsawa gwamnati kan janye shari’ar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da kuma maganar masarautun jihar Kano.”
“Masu shirya rigimar suna shirin kawo cikas a bukukuwan sallah a jihar da kuma zaman lafiyar da ake da shi a fadin jihar baki daya.”

Kara karanta wannan

Sauyin yanayi: Tsofaffin ma'aikata da matasa 10,000 za su samu aiki da gwamnatin tarayya

- Hussaini Gumel

Kwamishinan ya kara da cewa rundunar ta inganta tsaro a jihar da kuma saka idanu a wurare masu muhimmanci a birnin.

APC ta shawarci Abba kan binciken Ganduje

A baya, mun kawo muku cewa jam’iyyar APC a jihar Kano ta shawarci Gwamna Abba Kabir da ya fara bincikar Sanata Rabiu Kwankwaso a jihar.

Jam’iyyar ta ce madadin bata lokaci wurin binciken tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya kamata a bankado badakalar da Kwankwaso ya yi.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta kafa kwamitin binciken Ganduje musamman a badakalar kadarorin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel