Ramadan: Babban Limamin Abuja Ya Magantu Kan Kudin Shiga Itikafi da Masallatai Ke Karba

Ramadan: Babban Limamin Abuja Ya Magantu Kan Kudin Shiga Itikafi da Masallatai Ke Karba

  • Limamin babban masallacin kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, ya yi Allah wadai da kudin da Masallatai ke karba na shiga Itikafi
  • Shehin malamin ya ce karbar kudi domin yin ibada a Masallaci haramun ne, kuma bidi'a ce babba da ta zarce duk wata musiba ta zamani
  • Farfesa Maqari na martani ne kan N130,000 da wani Masallaci da ke Legas yake karba daga hannun masu shiga Itikafi cikin watan Ramadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Farfesa Ibrahim Maqari, babban limamin Masallacin Juma'a na kasa da ke Abuja, ya ce bidi'a ne Masallaci ya karbi kudi daga hannun masu shiga Itikafi.

Malamin addini ya magantu kan biyan kudi domin shiga Itikafi a Masallatai
Farfesa Maqari ya jaddada cewa bidi'a ce babba ace sai an biya kudi a yi ibada a Masallaci. Hoto: Prof. Ibrahim Maqari
Asali: Facebook

Farfesa Maqari na martani ne kan wani Masallaci a Legas da ya fito da wani tsari na sai mutum ya biya kudi sannan za a bar shi ya yi ibadar.

Kara karanta wannan

Lamunin karatu: Tsare-tsaren da gwamnati ta yi na fara ba dalibai rancen kudi

A yayin da ya ke gabatar da tafsirin Alkur'ani na watan Ramadan a babban Masallacin Abuja, malamin ya nuna bacin ransa tare da yin Allah wadai da matakin wancan Masallaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bidi'a ce karbar kudin" - Farfesa Maqari

Kamar yadda jaridar Aminiya ta rahoto malamin addinin ya yi nuni da cewa bidi'a ce mai muni da Masallacin na Legas suka aikata wanda ta zarce duk wata fitina ta zamani.

Farfesa Maqari ya kuma ce karbar kudi daga hannun masu ibadar Itikafi kan iya saukar da fushin Ubangiji a kan duniyar baki daya.

Babban limamin ya ce:

"Masallaci dakin Allah ne wanda kuma kowa ya sani wurin ibada ne ke dauke duk wani girma da matsayi na bayi domin su zamadaya yayin da suke ganawa da Allah.
"Cewar sai an biya kudi a shiga dakin Allah zai bude kofar nuna bambanci a tsakanin Musulmi wanda hakan ya sabawa koyarwar addini."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga masallaci sun dauke masallata ana sallar dare a Jihar Arewa

Halarcin biyan kudi a Masallatai

A yayin da ake gabatar da tambayoyi bayan kammala tafsirin, wani ya yi kokarin ankarar da malamin kan cewar Masallacin na karbar kudin ne domin gudanar da ayyukansa.

Farfesa Maqari ya mayar da martani da cewa:

"Karbar wannan kudi domin Musulmi za su shiga ibadar Itikafi laifi ne, haramun ne, har sai idan wasu dakuna ne aka ware da masu ibada za su biya domin su rika kwana a ciki.
"Ko kuma ace mutum zai biya kudi kafin yayi amfani da banɗakuna na Masallacin, domin kula da tsaftar wajen, wannan ya halatta."

Sai dai malamin ya kara jaddada cewa saka dokar biyan kudi kafin mutum ya shiga ibadar Itikafi da nufin takaita yawan mutane haramun ne.

Masallatai na karbar kudi a Legas

Jaridar Aminiya ce ta bayar da rahoton cewa wani Masallaci a Lekki, jihar Legas ya ƙaƙaba harajin N130,000 ga masu son yin ibadar Itikafi a Masallacin.

Kara karanta wannan

APC ta dauki zafi kan sharrin da aka yi wa Matawalle, ta gargadi PDP a Zamfara

An ruwaito cewa masallatai da dama a Legas na karbar kudi daga N10,000 zuwa N30,000 ko sama da hakan ga Musulman da ke son yin Itikafi a Masallatansu.

Sai dai N130,000 da Masallacin na Lekki ya ke karba a wannan shekarar ya zarce na ko ina, lamarin da ya jawo hankalin jama'a a ciki da wajen jihar.

"Biyan kudin fansa haramun ne" - Maqari

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa babban limamin Masallacin na Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari ya ce biyan kudin fansa ga masu garkuwa haramun ne a addini.

Farfesa Maqari ya kafa hujja da wani Hadisin Manzon Allah, wanda ya hana wani mutumi ya bari barawo ya kwaci kudinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel