Sharudan shiga Itikafi a kwanaki goma na karshen watan Ramadan

Sharudan shiga Itikafi a kwanaki goma na karshen watan Ramadan

Har a yanzu lokaci bai kure ba da ya kamata musulmi su zage dantse da ba da himma wajen gudanar da ibada a yayin da bai wuce sauran kwanaki 5 ko 6 ba mu yi bankwana da watan Azumin Ramalana na bana.

Koda mutum bai kasance ya dage da ibada ba a kwanakin da suka shude, a yanzu musulmi za su iya ribatar kwanakin da suka rage wajen tara dimbin lada.

A dage da rokon gafarar Ubangiji, nemansa da ya biya bukatu, sannan kuma a mika kai wajen yi masa ibada babu dare babu rana doriya a kan wadda aka saba yi a baya.

Hakika watan azumi wata ne mai girma wanda Allah {SWT} ya kebance shi da mafificin bauta a cikinsa, inda yace: “Azumi nawane, kuma ni kadai zanyi sakayya da shi”, kuma ya saukar da littafin sa mai girma acikin dare mai tsada na kwanuka masu falala na karshen watan.

Sharudan shiga Itikafi a kwanaki goma na karshen watan Ramadan
Sharudan shiga Itikafi a kwanaki goma na karshen watan Ramadan
Asali: UGC

Wanda a cikinsu Annabinmu Annabi Muhammad {SAW} ya kasance yana kara himma da dagewa wajen kusantar ubangijinsa.

Nana Aisha {RA} tana cewa: Manzon Allah {SAW} ya kasance idan goma karshe suka zo na Ramadan yana raya dare, ya kuma tashi iyalansa, ya dage, ya kara kaimi.

Daga cikin himma da dagewa da yake yi na goman karshen na Ramadanan shine: Yana kebance kansa daga iyalansa da sauran jama’a ya koma Masallaci (ITIKAFI).

Itikafi wata ibada ce da musulmai ke yi, a kwanaki na karshen watan Ramadana don neman lada da kuma kara kusanci izuwa ga Allah, domin koyi da fiyayyen halitta Annabi Muhammad {SAW}.

MENENE ITIKAFI:

Itikafi a shari’a shine lazumtar masallaci da tsayuwa a acikinsa da niyar kara kusanci zuwa ga Allah {SWT}.

Malamai sun hadu akan shar’ancin yin itikafi, saboda hadisin Nana Aisha {RA} tace: Manzon Allah {SAW} ya kasance yana yin itikafi a goman karshe na Ramadan har sai da ya koma zuwa ga Allah, sannan matan sa suka koma yi bayan sa.

Sannan uwar Muminan Aisha {RA} takara da cewa: Ya kasance idan yayi nufin itikafi sai yayi sallar Alfijir ta safiyar ranar ashirin, sannan sai ya shiga masallaci da niyar itikafi.

Shari’a ta nuna mutumin da zai iya yin wannan ibada ko sai ya kasance musulmi, kuma ya zama babu wani dangi na daga dangogi na janaba a tare da shi ko ita.

LADUBA GA MAI YIN ITIKAFI: Nana Aisha {RA} ta ce:

1. Ba zai je duba mara lafiya ba

2. Ba zai halarci jana’iza ba

3. Ba zai shafi ko rungumar mace ba

4. Ba zai fita daga masallacin ba sai da matsananciyar bukata

ABINDA YA HALARTA GA MAI ITIKAFI:

1. Fitowa domin ziyarar ahalinsa

2. Tsaftace gashin sa, yankan farce, tasaftar jiki, gami da shafa turare

3. Fitowa domin matsananciyar bukata (kamar kama ruwa,bayan gida d.s)

ABINDA YAKE WARWARE ITIKAFI:

1. Fitowa ba tare da wata bukata muhimmiya ba, da gangan

2. Gushewar hankali (hauka, ko maye)

3. Yankewar jinin al’ada ko kuma na biiki

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng