Watan Ramadan: Muhimman Abubuwan Yi a Cikin Ranaku 10 Na Karshe

Watan Ramadan: Muhimman Abubuwan Yi a Cikin Ranaku 10 Na Karshe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Watan azumin Ramadan wata ne mai alfarma da daraja ga al'ummar musulmi, inda suke ƙara neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar gudanar da ibadah da ayyukan alkhairi.

Musulmai na zage damtse tare da ƙara dagewa wajen gudanar da ibadah a cikin watan azumi domin samun rabauta da rahama, gafara da ƴantawa daga wutar jahannama daga wajen Allah maɗaukakin sarki.

Ayyukan yi a 10 karshe na Ramadan
Ranaku 10 na karshen cike suke da falala Hoto: @theholymosques
Asali: Twitter

Falalar da ake samu a watan ya sanya tun kafin ya shiga ake tunatarwa da jan hankali ga al'ummar musulmi da su dage da ibadah a cikinsa domin samun rabauta.

An keɓe kwanaki 10 na ƙarshen watan a matsayin waɗanda suka fi daraja da falala, inda ake ninka ladan da ake samu daga ayyukan ibadah da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar mutum 313 da ake zargi da aikata ta'addanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayyukan aka so a yi a 10 ta ƙarshen Ramadan

Legit Hausa ta tuntuɓi Sheikh Mustapha Salis Albamalli Zaria wanda ya yi bayani kan ayyukan da ake so a dage da gudanarwa a cikin kwanaki na ƙarshen watan Ramadan.

1. Karatun Al-Qur'ani

Yawaita karatun Al-Qur'ani mai girma na daga cikin abubuwan da aka so al'ummar musulmi su dage da yi a cikin kwanaki 10 ƙarshen Ramadan.

Karatun Al-Qur'ani a watan Ramadan yana da tarin lada mai yawa, kuma a cikin watan Ramadan aka saukar da littafin mai tsarki.

2. Sallar dare

A kwanaki 10 na ƙarshen watan Ramadan ana son a dage wajen yawaita sallar dare domin rabauta da samun lada.

Sallar dare na iya kai ga sanya wa a dace da riskar daren 'Lailatul Qadr' wanda darajarsa ta fi ta watanni 1000.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Abubuwan sani 5 dangane da jana'izar da za a yi wa jami'an tsaron

3. Sadaka

An so yawaita sadaka a cikin waɗannan kwanaki masu daraja. Sadaka na da lada sosai wanda yin ta a wannan lokacin zai sanya a samu lada mai tarin yawa.

4. Yawaita zikiri

A kwanakin ƙarshe na watan Ramadan an so a yawaita ambaton Allah maɗaukakin Sarki domin samun lada.

Yawaita salatin Annabi Muhammad (SAW) da istigfari na sanya wa a samu lada mai tarin yawa.

5. I'itikafi

Ana iya shiga I'itikafi domin shagaltuwa wajen bautar Allah a cikin waɗannan kwanaki masu falala da daraja mai girma.

Ramadan: Mutanen da ya halatta su ciyar

A wani labarin kuma, mun kawo muku mutanen da shari'a ta yadda su ciyar idan sun sha azumin watan Ramadan.

Shari'a dai ta yadda mutane biyu su ciyar idan sun sha azumi. Daga cikin mutanen da hukuncin ya hau kansu akwai tsohon da ya yi tsufar da ba zai iya komawa matashi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel