Sheikh Ibrahim Maqari ya yi Magana Game da Labarin 'zama' Limamin Masallacin Ka'aba

Sheikh Ibrahim Maqari ya yi Magana Game da Labarin 'zama' Limamin Masallacin Ka'aba

  • Babban limamin masallacin Najeriya da ke garin Abuja, Ibrahim Ahmed Maqari ya tanka rade-radin da ke yawo tun jiya
  • Rahotannin karya sun nuna Farfesa Ibrahim Ahmed Maqari ya zama daya daga cikin masu limanci a masallacin harami
  • Shehin yace bai san daga ina labarin ya fito ba, amma ya nuna cewa labarin bai wuce kyakkyawan zato da fatan alheri ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ibrahim Ahmed Maqari ya yi magana a kan jita-jitar da ta rika yawo daga ranar Lahadi, 21 ga watan Agusta 2022, na cewa an ba shi limancin harami.

Legit.ng Hausa ta fahimci Farfesa Ibrahim Ahmed Maqari ya maida martani ne a shafinsa na Twitter watau @ProfMaqari, ya nuna labarin nan ba gaskiya ba ne.

Tun da aka wayi a gari a jiya, Shehin malamin yace an yi ta kiransa a wayar salula a game da wannan labari da ya karada shafukan sada zumunta na zamani.

Kara karanta wannan

Shiga siyasa: Matasa a Abuja sun kama wani Bishap, sun lakada masa dukan tsiya

Ko da labarin ya bazu, babban limamin masallacin Abujan yace bai san tushen jita-jitar ba.

Ibrahim Maqari ya yi wa masu yada labarin kyakkyawan zaton suna yi ne da fatan alheri, ko kuma an samu kamanceceniyar suna, wanda hakan mai yiwu ne.

A karshen jawabin da ya yi a shafin na sa da kimanin karfe 1:20 na rana, shehin ya nuna matukar godiyarsa ga masoyansa da ke yi masa irin wannan fatan alheri.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sheikh Ibrahim Maqari
Jawabin Sheikh Ibrahim Maqari
Asali: Twitter

Abin da Farfesa Ibrahim Ahmed Maqari ya fada a Twitter

"Mutane suna ta kira akan wani labari da muka tashi da shi yau akan limancin masallacin Haram..
Kila dai fatan alkhairi ne ya sanya wadanda suka kirkiri labarin kirkirarsa ko kuma sunaye ne suka yi kama.
Muna matukar godiya da dukkan kyawawan zato da fatan alkhairi daga masoya."

Kara karanta wannan

Kamar almara: Sauyawar wani matashi daga sana'ar acaba zuwa tauraro ya ba da mamaki

A wani jawabi da ya yi a Ingilishi a shafin na sa duk a ranar Lahadi, malamin ya musanya wannan batu, ba tare da karyata masu yada shi ba.

“Mun tashi da labarin nadin Limamcin Masallacin Harami a Makkah…
Ko da ba mu san daga ina aka dauko wannan labari ba, babu mamaki kyakkayawan zato ne da fatan alheri daga masoya ko kuma an yi kicibis, sunaye su zo daya.
Mun gode da dukkanin addu’an masoya."

Su wanene za su kashe Dogara

An ji labari tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya ya rubuta takarda zuwa ga IGP, ya ankarar da ‘Yan sanda cewa akwai masu neman kashe shi.

A jiyan nan sai ga Kwamishinan Yan Sanda na Bauchi ya bayyana cewa daga cikin wadanda suke so su hallaka Yakubu Dogara, wani ya shigo hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel