Ziyarar El-Rufai Zuwa Jam’iyyar SDP Ba Zai Girgiza Tinubu Ba, Jigon APC Ya Yi Bayani

Ziyarar El-Rufai Zuwa Jam’iyyar SDP Ba Zai Girgiza Tinubu Ba, Jigon APC Ya Yi Bayani

  • Wani jigon APC, Francis Okoye, ya mayar da martani kan ziyarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya kai wa jam’iyyar SDP
  • Okoye ya ce ko kadan jam’iyyar APC ba ta da wata damuwa da ziyarar domin matakin zai kara raunana jam’iyyun adawa ne kawai a kasar
  • A zantawarsa da Legit.ng, ya ce idan El-Rufai ya bar APC ya koma SDP, jam’iyya mai mulki da kuma Bola Ahmed Tinubu za su yi nasara a 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja – Shugaban gamayyar kungiyoyin jam’iyyar APC na shiyyar Kudu-maso-Gabas, Francis Okoye, ya ce babu abin damuwa kan ziyarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya kai sakatariyar jam’iyyar SDP.

Kara karanta wannan

APC ta dauki zafi kan sharrin da aka yi wa Matawalle, ta gargadi PDP a Zamfara

Jigon APC ya yi magana kan ziyarar da El-Rufai ya kai wa jam'iyyar SDP
Zaben 2027: Francis Okoye ya ce Tinubu da APC ba za su damu da tafiyar El-Rufai ba. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

Okoye ya ce babu wanda ya san ko El Rufa'i na son ficewa daga APC amma idan har hakan ta tattaba, ya ce jam'iyyar ba ta da wata asara.

Me ziyarar El-Rufai zuwa SDP ke nufi?

Ya ce ziyarar da El-Rufai ya kai jam’iyyar SDP ya taimaka ne wajen kara raba kan ‘yan adawa da kuma karfafa jam’iyyar APC mai mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi a ranar Lahadi, 31 ga watan Maris.

“Tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya yi kira da kada a ji tsoro kan ziyarar da tsohon Gwamna El Rufa’i ya kai a sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa.
"Mu a APC babu abin da ya dame mu, sai dai hakan ya kara mana karfi a jam’iyya. Ziyarar za ta kara raba kawunan ‘yan adawa maimakon kara musu karfi”

Kara karanta wannan

Rikicin El-Rufai da Uba Sani: APC ta dauki mataki kan shugabar matan jam'iyyar

Wacce riba APC za ta samu a ziyarar?

Okoye ya zana hoton yadda za ta kasance idan aka ce El-Rufai ne dan takarar shugaban kasa na SDP, Sanata Rabiu Musa Kwakwanso a NNPP, Peter Obi a LP da kuma Atiku Abubakar a PDP.

Ya ce idan har hakan ta tabbata a zaben 2027, to ba makawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC za su samu gagarumar nasara.

El-Rufai vs Uba Sani: Akwai matsala?

Okoye ya ce rikicin da ya barke tsakanin El-Rufai da Gwamna Uba Sani ba zai yi wa al’ummar jihar Kaduna dadi ba.

Ya kuma gargadi bangarorin biyu da su mayar da makaman yakinsu domin ci gaban jihar Kaduna.

Dalilin zuwan El-Rufai sakatariyar SDP - Modibbo

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani jigon jam'iyyar APC, Dr. Ibrahim Modibbo ya ce ziyarar da Nasiru El-Rufai ya kai sakatariyar jam'iyyar SDP sharar fage ne na zaben 2027.

Dr. Modibbo ya ce jam'iyyar APC ta yi watsi da El-Rufai, wannan ya sa yake tunanin tsohon gwamnan jihar Kaduna ya fara nema wa kansa mafita tun kafin zaben ya zo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel