Rikicin El-Rufai da Uba Sani: APC Ta Dauki Mataki Kan Shugabar Matan Jam’iyyar

Rikicin El-Rufai da Uba Sani: APC Ta Dauki Mataki Kan Shugabar Matan Jam’iyyar

  • Yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan ikirarin Gwamna Uba Sani kan basukan jihar Kaduna, matsalar ta fara sauya salo
  • Jam'iyyar APC a jihar ta dakatar da shugabar mata na jam'iyyar bayan ta goyi bayan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai
  • APC ta dakatar da Maryam Suleiman har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan lamarin da ya jawo dakatar da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shugabar matan jam'iyyar, Maryam Suleiman.

Jam'iyyar ta dauki matakin ne saboda caccakar Gwamna Uba Sani da ta yi bayan ya yi zargin gadan bashi a jihar.

Kara karanta wannan

Ganduje ya karbi sabbin tuba bayan tsohon Sanata da Ministan PDP sun koma APC

APC a Kaduna ta dauki mataki kan shugabar mata game da rikicin El-Rufai da Uba Sani
APC ta dakatar da shugabar mata kan rikicin El-Rufai da yaronsa, Uba Sani. Hoto: Nasir El-Rufai, Maryam Suleiman, Uba Sani.
Asali: Facebook

Musabbabin dakatar da shugabar mata a Kaduna

Ana kuma zargin Maryam ta tura 'yan bangar siyasa domin kai hari kan hadimin gwamnan jihar a bangaren siyasa, Manzo Maigari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar a yau Lahadi 31 ga watan Maris, cewar Channels TV.

Sanarwar da shugaban jam'iyyar, da sakatarensa a Badarawa da Malali suka fitar, sun sanar da dakatarwar kan sukar Gwamna Uba Sani.

Matakin da jam'iyyar ta dauka a Kaduna

Jam'iyyar ta ce abin da Maryam ta aikata ya sabawa dokar jam'iyyar inda ta dakatar da ita har sai an kammala bincike kan lamarin.

A cikin wani a hira da DCL Hausa, an gano shugabar mata cikin harshen Hausa ta na caccakar gwamnan kan bashin da ya ce tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ya bar masa.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Uba da dansa sun yi taron dangi, sun yiwa matar makwabcinsu duban mutuwa a Ogun

Jam'iyyar ta ce daga yau Lahadi 31 ga watan Maris ta yanke shawarar dakatar da Maryam Suleiman da aka fi sani da Mai Rusau har sai bayan kammala bincike.

Uba Sani ya yi katobara kan bashi a Kaduna

A baya, mun ruwaito muku cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta gaji tulin bashin kudi da ayyuka daga gwamnatin Nasir El-Rufai.

Gwamn ya bayyana halin da gwamnatin Kaduna ta ke ciki, ya ce su na fama da biyan bashin kudin da aka karbo a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel