Sojoji sun kama makiyaya 10 suna barna a cikin wata gona a jihar Benuwe
- Rundunar sojojin attisayen ‘Gudun muzuru sun kama makiyaya 10 suna barna a cikin wata gona a jihar Benuwe
- Sojoji sunce sun samu lauyoyi, babura da N120,000 a hannun makiyayan da suka kama suna barna a cikin wata gona
Dakarun sojojin da aka tura gudanar da attisayen ‘Gudun muzuru ‘ a yankin Arewa ta tsakiya sun kama makiyaya guda goma suna ta’adi a cikin wata gona dake kauyen Tse-Tigir a jihar Benuwe a ranar Litinin.
A jawabin da kakakin rundunar sojojin Najeriya, Brigediya Janar Texas Chukwu, ya fitar yace, masu laifin sun gudu cikin daji yayin da suka ga sojoji suna zuwa a lokacin da suke barna a cikin wata gona.
“Dakarun sojojin sun bi su a lokacin da suka ga makiyayan sun fice aguje kuma sun samu nasarar kama su,” inji si.
KU KARANTA : Dattawan yankin Kudu da na Arewa ta tsakiya sun gargadi Buhari akan sanya dokar ta baci a jihar Benuwe
An samu Babura guda biyar, adduna guda biyu, lauyoyi da N120,000 a hanun su.
Chukwu ya ce sun mika masu laifin tare da abubuwan da aka kwato a hannun su zuwa wajen ‘yansanda dan cigaba da bincke.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng