Kungiya Ta Yi Magana Kan Zargin da Ake Yi Wa Ministan Tinubu Na Ba 'Yan Bindiga Tallafin Abinci

Kungiya Ta Yi Magana Kan Zargin da Ake Yi Wa Ministan Tinubu Na Ba 'Yan Bindiga Tallafin Abinci

  • Wata ƙungiya a Arewacin Najeriya ta yi kakkausar suka ga gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, inda ta zarge shi da yin watsi da matsalolin tsaron da jihar ke fuskanta
  • Sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda bidiyoyi suke yawo a shafukan sada zumunta inda ƴan bindiga ke fitowa fili suna yabon gwamnan
  • Ƙungiyar ta yi Allah-wadai da shugabancin Lawal, inda ta ce bai san inda ya dosa ba kuma ya taimaka wajen ƙara taɓarɓarewar tsaro a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar Arewa Youth for Peace and Security ta yi kakkausar suka kan gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, inda ta zarge shi da yin watsi da al’amuran tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ya faɗawa manyan Malamai da Sarakuna a wurin buɗa baki a Aso Villa

Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun ce tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro a yanzu, Bello Matawalle, ya bayar da tallafin abinci ga ƴan bindigan da Ado Aliero ke jagoranta.

Kungiya ta caccaki Gwamna Dauda Lawal
An zargi Matawalle da ba 'yan bindiga tallafin abinci Hoto: Bello Matawalle, Dauda Lawal
Asali: Facebook

Ƙungiyar ta yi zargin cewa Lawal ya zuzuta matsalar tsaro lokacin Matawalle domin samun goyon baya amma ya kasa cika alƙawuran da ya ɗauka na magance matsalar yanzu da yake kan mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dauda Lawal ya kasa magance rashin tsaro

A wata sanarwa da ƙungiyar ta rabawa Legit.ng a ranar Asabar, 30 ga watan Maris, ta ce:

"Tun bayan da Lawal ya hau kan mulki, ya kasa samun hanyar da zai magance matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar.
"Abin takaici ne Gwamna Lawal wanda ya yi amfani da matsalar rashin tsaro a Zamfara a matsayin farfaganda domin yaudarar mutane cewa zai dawo da tsaro cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya samo mafita kan hanyar kawo karshen 'yan bindiga a Arewacin Najeriya

"Yanzu ya yi watsi da su yayin da yake ta yawace-yawacensa a faɗin duniya ya bar aikin da ya rataya a wuyansa na samar da romon dimokuraɗiyya ga ƴan jihar.
"Domin ya wanke kansa, Lawal ya mayar da hankali wajen wawushe dukiyar al'umma, ɗaukar nauyin yaɗa ƙarya da ƙarairayi a kan Matawalle, domin ya samu suna da tausayi daga mutanen Zamfara."

Ƙungiya ta caccaki gwamnan Zamfara

Ƙungiyar ta caccaki Gwamna Lawal, inda ta yi zargin cewa shugabancinsa a jihar Zamfara ba shi da alƙibla kuma ya janyo taɓarɓarewar tsaro.

Sun koka kan yawaitar faifan bidiyo a shafukan sada zumunta inda bindiga ke fitowa fili suna yaba wa gwamnan, wanda hakan ke nuna cewa jihar ta zama matattarar masu aikata laifuka.

Ƴan bindiga sun kashe limami

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Zamfara.

A yayin harin, ƴsn bindiga sun hallaka babban limamin masallacin Juma'a na ƙauyen Keita da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel