'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Zamfara, Sun Hallaka Babban Limami, Sace Mutane Masu Yawa

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Zamfara, Sun Hallaka Babban Limami, Sace Mutane Masu Yawa

  • Sheikh Ahmad Rufa'i, limamin babban masallacin Juma'a na ƙauyen Keita a jihar Zamfara, ya gamu da ajalinsa yayin wani harin da ƴan bindiga suka kai
  • A cewar Ibrahim Musa Keita, wani mazaunin ƙauyen, lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala sallar Isha'i
  • Miyagun sun kuma yi awon gaba da mutane masu yawa waɗanda ba a tantance adadinsu ba ciki har da mata a yayin harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Tsafe, jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga sun halaka Sheikh Ahmad Rufa'i, babban limamin masallacin Juma'a da ke ƙauyen Keita a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Kisan Sheikh Rufa’i ya faru ne makonni uku kacal bayan kisan da aka yi wa Imam Abubakar Hassan Mada, babban limamin masallacin Juma’a na Mada, da ke ƙaramar hukumar Gusau a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya samo mafita kan hanyar kawo karshen 'yan bindiga a Arewacin Najeriya

'Yan bindiga sun hallaka limami a Zamfara
'Yan bindiga sun kai sabon harin ta'addanci a Zamfara Hoto: @Daudalawal
Asali: Twitter

A cewar Ibrahim Musa Keita, wani mazaunin Keita, ƴan bindigan sun kai farmaki ƙauyen ne jim kadan bayan kammala sallar Isha’i, cewar rahoton jaridar Sahara Reporters.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Jaridar Daily Trust ta ambato shi yana cewa:

"Kafin a kai farmakin, an sanar da mazauna ƙauyen wucewar ƴan bindiga kan hanyar Kwarin Gano-Keita.
"An gansu a kan hanyar amma ba mu da tabbacin ko za su zo wannan ƙauyen ko a'a.
"Da farko sun so su yi awon gaba da matafiya a kan hanyar Keita zuwa Kwarin Gano, amma bayan sun ɗauki lokaci ba tare da samun ko mutum ɗaya ba, sai suka farmaki ƙauyen Keita, suka kashe babban limaminmu tare da sace mutane da dama ciki har da mata.
"Ba mu tantance adadin mutanen da suka yi garkuwa da su ba yayin da wasu suka tsere cikin daji har yanzu ba a gansu ba.”

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya fadi yadda gwamnatin Tinubu za ta yi nasara

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Abubakar Yazid, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Sai dai, kakakin ya bayyana cewa a halin yanzu ba ya cikin jihar, ya yi wata tafiya, amma zai bincika lamarin domin bada bayanai.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba a ji daga gare shi ba.

Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Baure da ke ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun halaka mutum biyu yayin harin bayan sun buɗe wuta kan mai uwa da yabi lokacin da mutane ke yin buɗa baki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel