Abin da Bola Tinubu Ya Faɗawa Manyan Malamai da Sarakuna a Wurin Buɗa Baki a Aso Villa

Abin da Bola Tinubu Ya Faɗawa Manyan Malamai da Sarakuna a Wurin Buɗa Baki a Aso Villa

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi buɗa bakin azumi na 18 tare da manyan malamai da sarakuna a fadar shugaban kasa ranar Alhamis
  • Shugaban ƙasar ya roƙi malamai su guji zagin Najeriya a wurin wa'azi domin kasar ta su ce kuma addu'a ta fi buƙata
  • Tinubu ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta kudiri aniyar sauya kalubalen da Najeriya ke fama da su zuwa nasara da wadata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga malaman addini da su guji zage-zage ko cin mutuncin ƙasar nan a wa’azin da suke yi.

Tinubu ya faɗi haka ne yayin buɗe baki tare da sarakunan gargajiya da manyan malaman addinai daban-daban a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya bayyana hanyar da ƴan adawa za su iya tsige shi daga mulki

Bola Ahmed Tinubu.
Tinubu ya ja hankalin malamai su guji la'antar Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajure Ngelale ya fitar ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya jaddada muhimmiyar rawar da malamai ke takawa wajen tsara ra'ayoyin jama'a da kuma samar da hadin kai a tsakanin 'yan kasa.

Bola Tinubu ya roƙi malamai da sarakuna sun san me zasu faɗa yayin sukar zaɓaɓɓun shugabanni, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kudiri aniyar kawo sauyi.

Abin da Tinubu ya faɗawa malamai da sarakuna

Ya bukaci sarakuna da na malamai su ƙulla alaka mai karfi da gwamnati domin daƙile ayyukan ta’addanci, ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a kasar nan.

"Ku yi wa ƙasar nan addu'a, ku wayar da kan yaranmu, wa'azozin da kuke yi a coci-coci da masallatai suna da muhimmanci, ku daina la'antar ƙasar nan taku."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauko ɗan Arewa, ya naɗa shi a babban muƙami a watan azumi

"Wannan ƙasar ku ce, ku daina tir da ita a gaban jama'a a wurin wa'azi, ku guji zagin Najeriya, shi shugabanci abu ne da za a iya sauyawa.
"Idan shugaba ba mutumin kirki bane, ku jira zaɓe na gaba ku sauya shi amma ku daina la'antar ƙasar ku, kada ku zage ta, kyakkyawar ƙasa ce."

- Bola Tinubu.

Babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani ya wallafa wannan sanarwa a shafinsa na manhajar X watau Twitter.

Tinubu ya naɗa shugaban CCB

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Dakta Abdullahi Bello a matsayin sabon shugaban hukumar ɗa'ar ma'aikata ta ƙasa (CCB).

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, 2024

Asali: Legit.ng

Online view pixel