Rikici a Plateau: An kashe mana mutum 70 cikin kwanaki 4, Mutan Irigwe

Rikici a Plateau: An kashe mana mutum 70 cikin kwanaki 4, Mutan Irigwe

  • Kungiyar mutan Irigwe sun yi ikirarin cewa yan bindiga sun kashe musu mutum 70
  • Rikici a Pleteau kwanakin baya ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya
  • Gwamnatin Plateau ta ce an kwantan da kuran yanzu

Plateau - Akalla mutum 70 ne aka ce sun rasa rayukansu a garin Jebbu Miango da Kwall na karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau sakamakon harin yan bindiga.

Kaakin kungiyar cigaba Irigwe, Davidson Malison, ya bayyana hakan ranar Alhamis yayinda yan ziyara suka ziyarci wajen da aka kai harin.

Ya ce an kashesu ne lokacin hare-haren da aka kwashe kwanaki hudu tun ranar Asabar zuwa Laraba ba tare da taimakon yan sanda ko wasu jami'an tsaro ba.

Malison yace an kona sama da gidaje kimanin 3000, daga ciki har da gidan tsohon dan majalisa Hon Lumumba Da'ade da kayan abinci, janareto, babura, kuma aka sace injinan ruwa.

Ya yi bayanin cewa yan bindigan Fulani Makiyaya ne suka shiga garin cikin motoci.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin jama'an gari da yan Shi'a a jihar Kano

Yace:

"Cikin kwanaki hudu, sama da mutane 70 aka kashe, an kona gidaje 2500, an kona gonaki hekta 1000.
"Wadannan makiyayan sun kwashe dabbobi na kimanin kudi N100m. Wannan shine karo na farko da garin Irigwe zai fuskanci irin wannan hari.

Rikici a Plateau: An kashe mana mutum 70 cikin kwanaki 4, Mutan Irigwe
Rikici a Plateau: An kashe mana mutum 70 cikin kwanaki 4, Mutan Irigwe
Asali: Twitter

Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane

Wasu yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kai hari wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Bassa, jihar Filato, kamar yadda punch ta ruwaito.

Yayin harin yan bindigan sun hallaka mutum huɗu tare da ƙona gidajen mutane da dama, kamar yadda this day ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa harin, wanda ya bar mutane da dama cikin raunuka, ya faru ne lokacin mutane na bacci ranar Asabar da daddare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel