Albarkacin Watan Radaman, Musulmi Ya Taimakawa Coci da N1m da Bulo 2,000 a Jos

Albarkacin Watan Radaman, Musulmi Ya Taimakawa Coci da N1m da Bulo 2,000 a Jos

  • Yayin da ake ci gaba da azumin watan Ramadan, wani attajiri a garin Jos ya taimakawa coci da makudan kudi
  • Injiniya Huzaifa Ibrahim Abdullahi ya ce ya ba cocin kyautar N1m da kuma bulo guda 2,000 domin gina cocin
  • Legit Hausa ta ji ta bakin aramma kuma malamin addini game da mahangar Musulunci kan wannan kyauta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau – Wani attajiri a birnin Jos da ke jihar Plateau, Injiniya Huzaifa Ibrahim Abdullahi ya bukaci Musulmai da Kirista su hada kai domin zaman lafiya.

Huzaifa ya ce zaman lafiya ne kadai zai kawo ci gaba a Jos dama jihar baki daya wacce ta sha fama da rikice-rikice, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya bayyana hanyar da ƴan adawa za su iya tsige shi daga mulki

Musulmi a Jos ya ba coci gudunmawa makudan kudi albarkacin Ramadan
Attajiri a Jos ya taimakawa coci da N1m da kuma bulok 2,000 domin inganta zaman lafiya. Hoto: Asanduff Company, Christianity.com.
Asali: UGC

Dalilin ba da gudunmawa ga coci

Attajirin ya bayyana haka ne a coci da ke Tahir a Jos yayin da ya ke ba da gudunmawar N1m da kuma bulo 2,000 ga cocin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya ba da wannan gudunmawa ne domin ci gaba da gina sabon sashe na cocin a wani bangare da ke birnin Jos.

“Na fahimci wasu su na gudanar da bauta a cikin langa-langa sai naga hakan bai dace ba ya kamata a gina wani coci a wani wuri.”
“Na yanke shawara ba da gudunmawar bulo 2,000 da kuma kyautar N1m domin fara gina wani sabon coci.”

- Huzaifa Ibrahim

Daga bisani attajirin ya bukaci al'ummar Musulmai da Kirista da su hada kai domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Sakataren cocin, Mista Tevzing Ndeh ya godewa Injiniya Huzaifa da irin wannan taimako da ya kawo wa cocin.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Sanata ya dauki zafi kan karin kudin kujera, ya fadawa Tinubu abin da zai yi

"Abin da ka yi zai taimaka wurin kawo zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mutane."
"Ya kamata mu ci gaba da gudanar da abubuwa da za su kara zaman lafiya a tsakaninmu, mun yi godiya matuka da wannan gudunmawa."

- Tevzing Ndeh

Aikata hakan ya haramta a Musulunci

Legit Hausa ta ji ta bakin aramma kuma malamin addini game da mahangar Musulunci kan wannan kyauta

Mallam Idris Abdallah Idris da ke Gombe ya ce gaskiya hakan bai dace ba a .

Ya ce idan wani taimako ne da ya shafi gidajensu babu laifi amma ya haramta Musulmi ya ba da gudunmawa wurin ibadar wadanda ba Musulmai ba.

"Ko da aikin lada ne a coci haramun ne tun da ba gidajensu ba ne, saboda za ka iya ba wanda ba Musulmi ba gida wanda ke karkashinka domin nuna adalcin Musulunci ko zai Musulunta."
"Wannan abin da ya yi haramun ne saboda ubangji zai tambaye shi yadda ya kashe kudinsa a lahira kaga shi kuma ya taimaka musu wurin ibadarsu."

Kara karanta wannan

Tudun Biri: An fara muhimman ayyuka 3 a ƙauyen da sojoji suka yi kuskuren jefa bam a taron Maulidi

- Idris Abdallah Idris

Omokri ya ba Obi shawara kan Musulmai

Kun ji cewa Reno Omokri ya ba dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi shawarar yadda Musulmai za su zabe shi.

Omokri ya ce zai wahala al'ummar Musulmai su zabe shi idan har bai ba su hakuri kan furta kalaman da ya yi a zaɓen 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel