2027: Al'ummar Musulmai Ba Za Su Taɓa Zabar Obi Ba, Reno Omokri Ya Bayyana Dalilai

2027: Al'ummar Musulmai Ba Za Su Taɓa Zabar Obi Ba, Reno Omokri Ya Bayyana Dalilai

  • Yayin da Peter Obi ke ci gaba da ziyartar Musulmai a wannan azumi, Reno Omokri ya ba shi shawara kan zaben 2027
  • Omokri ya ce madadin yawace-yawacen da ya ke yi, da neman afuwarsu ya yi kan abin da ya fada a zaben 2027 zai fi samun shiga
  • Wannan na zuwa ne yayin da dan takarar shugaban kasa a LP ke yawan ziyartar masallatai tare da buda baki da Musulmai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Reno Omokri ta ba dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi shawarar yadda Musulmai za su zabe shi.

Omokri ya ce zai wahala al'ummar Musulmai su zabe shi idan har bai ba su hakuri kan furta kalaman da ya yi a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Abacha ya karkatar da maƙudan kudi a mulkinsa? Buba Galadima ya fayyace gaskiya

Omokri ya fadi abin da Obi zai yi ya karbu a wurin Musulmai
Reno Omokri ya shawarci Peter Obi yadda zai shawo kan Musulmai. Hoto: Reno Omokri, Peter Obi.
Asali: Facebook

Wace shawara Omokri ya ba Obi?

Reno ya bayyana haka a yau Lahadi 24 ga watan Maris a shafinsa na X inda ya ce dole Obi ya roki gafarar Musulmai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina yabawa Obi kan yadda ya ke ziyartar Musulmai, idan ya na son gyara tsakaninsa da su ba kawai buda baki a nan da can ba ne, kamar yadda ya ce coci za ta karbi mulki a zaben 2023."
"Na san Musulmai sosai, akwai yafiya a cikin Musulunci , idan ya amince muryarsa ce kuma ya nemi afuwa a wurinsu da yafi saboda na san za su yafe masa."

- Reno Omokri

Ya ce Musulmai za su ba Obi mamaki

"Musulmai za su yi buda baki da shi ba tare da matsala ba, amma a 2027 zai tabbatar ba su manta ba, babu tafiya ba tare da tuba ba."

Kara karanta wannan

Gaskiya ta bayyana: Jigon LP ya bayyana dalilin da yasa Peter Obi ya yi buda-baki da Musulmai

- Reno Omokri

Omokri ya ce al'ummar Musulmai ba za su taɓa zabar mutumin da ya nuna zai yaƙe su ba a matsayin shugaban kasa ko mataimaki.

Obi zai yi haɗaka da El-Rufai

A baya, mun ruwaito muku cewa na hannun daman Atiku Abubakar, Daniel Bwala ya bayyana yiwuwar hadewar Peter Obi da Nasir El-Rufai.

Bwala ya ce alamu sun tabbatar da cewa Obi zai bar jami'yyarsa ta LP yayin da kungiyar NLC ke neman kwace ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel