Addu’a Ce Za Ta Kawo Karshen Rashin Tsaro a Najeriya, Shugaban Sojin Ruwan Najeriya

Addu’a Ce Za Ta Kawo Karshen Rashin Tsaro a Najeriya, Shugaban Sojin Ruwan Najeriya

  • Shugaban sojin ruwan Najeriya ya ce addu'a ce za ta kawo mafita ga matsalar tsaro da tattalin arziki a Najeriya
  • Ya yi tsakaci ga manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta da kokarin da shugaban kasa ke yi don warware su
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da kuka kan yadda kasar ke ci gaba da tabarbarewa ta fannoni da yawa a yanzu

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - Babban hafsan sojin ruwan Najeriya, Vice Admiral Emmanuel Ogalla, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su dukufa da addu’ar zaman lafiya, hadin kai da kuma ci gaba wajen fuskantar kalubalen da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Tinubu ya roki 'yan Najeriya hanya 1 da za su inganta darajar naira da kansu cikin sauki

Ya ce duk da cewa kasar nan na fuskantar kalubale masu tarin yawa ta fuskar tattalin arziki da tsaro, ya ce idan aka dukufa da addu’a, Allah zai ba da mafita.

Addu'a ce mafita ga matsalolin Najeriya, shugaban sojin ruwa
Shugaban sojin ruwa ya ce addu'a za ta kawo maganin rashin tsaro | Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Ya yi wannan batu ne a wani taron buda-baki da hukumar kula da harkokin addinin musulunci ta Najeriya ta shirya a azumin watan Ramadan na bana a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku koma ga Allah, shugaban soji ga 'yan Najeriya

A cewarsa, duba da kalubalen zamantakewa da tattalin arziki a Najeriya, akwai bukatar ‘yan kasa su jajirce wajen neman taimakon Allah, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa:

"Ina kira ga 'yan uwa musulmi da su ci gaba da yiwa wannan kasa addu'ar zaman lafiya da dawwamar tsaro."

Tinubu na kokarin magance matsalolin trsaro

A bangare guda, shugaban na sojin ruwa ya bayyana irin kokarin da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ke yi wajen ganin an samu wanzuwar zaman lafiya a Najeriya, Politics Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zamfara: Tsohon Sanata ya fadi hanyar kawo karshen matsalar tsaro har abada

Hakazalika, ya ce ya kamata 'yan Najeriya su koma ga Allah tare da sanya shugabanni a addu'o'i wajen ganin sun yi aikin da ya rataya a wuyansu.

Matsalar tsaro da tattalin arziki ne manyan abubuwan da suke damun 'yan Najeriya, kuma har yanzu ba a samu mafita ba.

Ku koma ga Allah, Gowon ya shawarci 'yan Najeriya

A wani labarin, Yakubu Gowon, tsohon shugaban kasa na mulkin soja, ya roki 'yan Najeriya da su cigaba da kasancewa masu kishin kasa duk da matsalar rashin tsaro dake addabar kasar.

Ya ce lamarin wani bangare ne kawai wanda kasar za ta shawo kansa a karshe, musamman idan aka dukufa.

Gowon yayi magana ne a ranar Asabar a wajen bikin cika shekaru 23 ta Peace Corps of Nigeria (PCN) a Abuja, inda ya samu wakilcin Chris Garba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel