Gowon: Ku koma ga Allah, rashin tsaro zai kare a Najeriya nan kusa, ya bayyana mafita
- Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, Yakubu Gowon ya bukaci 'yan Najeriya su koma ga Allah
- Ya bayyana cewa, matsalolin da Najeriya suke fuskanta ba za su tabbata har abada a Najeriya ba
- Ya ce nan kusa matsalolin za su kare idan 'yan Najeriya suka zama masu kishin kasa da son kasar
Yakubu Gowon, tsohon shugaban kasa na mulkin soja, ya roki 'yan Najeriya da su cigaba da kasancewa masu kishin kasa duk da matsalar rashin tsaro dake addabar kasar.
Ya ce lamarin wani bangare ne kawai wanda kasar za ta shawo kansa a karshe.
Gowon yayi magana ne a ranar Asabar a wajen bikin cika shekaru 23 ta Peace Corps of Nigeria (PCN) a Abuja, inda ya samu wakilcin Chris Garba.
KARANTA WANNAN: Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna
Jaridar Sun ta ruwaito yana cewa:
“Yanayin rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da yanayin rashin kwanciyar hankali ba zai dawwama ba har abada; yanayi ne mai wucewa.
'Yan Najeriya su koma ga Allah da gwamnati
Ya bukaci ‘yan Najeriya su yi addu’a tare da marawa gwamnati baya a yaki da rashin tsaro, hare-hare ba kakkautawa da satar mutane.
Ya ce:
“Ina ganin ya kamata mu yi wa shugabanci addu’a. Ya kamata mu yi wa mutanenmu da hukumomi dama cibiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu addu’a kada su karaya, ya kamata su ci gaba da yin iya kokarinsu kuma su ci gaba da mai da hankali don ganin cewa burin kasar ya cika."
KARANTA WANNAN: Murna: Hotunan Atiku da Daya Daga Cikin 'Yan Matan Chibok Lokacin da Ta Kammala Digiri
A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da ake zargin 'yan fashi ne sun harbe wasu jami’an hukumar shige da fice ta kasa (NIS) har mutum biyu a cikin jihar Katsina.
An bayyana sunayen jami’an da Umar Bagadaza Kankara da Lauwali Dutse.
Lamarin wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Alhamis da misalin karfe 12:05 na safe, ya faru ne a kauyen Kadobe, dake karamar hukumar Jibia.
Asali: Legit.ng