Lai: ‘Soshiyal Midiya’ Ya Kusa Raba Auren Minista da Matarsa Bayan Shekaru 40 Tare

Lai: ‘Soshiyal Midiya’ Ya Kusa Raba Auren Minista da Matarsa Bayan Shekaru 40 Tare

  • Farfesa Wole Soyinka ya cika shekaru 90, sai aka gayyato Lai Mohammed a cikin wadanda suka yi jawabi a wajen biki
  • Tsohon Ministan yada labarai da al’adun ya bada labarin yadda labaran bogi maras tushe suka jefa shi a cikin matsala
  • Lai ya ce matarsa ta taba biyewa labarin karya da aka rika yadawa na cewa yana da hannu a badakalar Dala biliyan 1.3

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Lagos - Lai Mohammed wanda ya yi Ministan yada labarai da al’adu na kasa, ya yi magana game da illolin dandalin sada zumunta.

Alhaji Lai Mohammed ya bada labarin yadda kafofin sadarwa na zamani suka nemi su kawo masa barazana har cikin gidan aurensa.

Lai Mohammed
Soshiyal Midiya ya kusa raba auren Lai Mohammed Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP, Shannon Finney
Asali: Twitter

Lai Mohammed ya ga illar soshiya midiya

The Cabla ta ce tsohon Ministan ya yi jawabi ne a Legas inda aka shirya biki domin taya Farfesa Wole Soyinka murnar cika shekara 90.

Kara karanta wannan

Mun tada matattu sama da 50 a cocina bayan tabbatar da mutuwarsu, inji malamin coci Chris

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar ya ce a lokacin da yake ministan tarayya, daga cikin kalubalen da ya fuskanta su ne mugun tasirin labaran bogi da karya.

Lai yake cewa mummunan tasirin shafukan sada zumuntan ya shiga cikin gidan aurensa, ya kusa kashe masa auren shekaru 40.

Labarin Lai a kan illar soshiya midiya

"Ina neman izininku a yau, a karon farko in ba da labarin yadda dandalin sada zumunta ya kusa rusa tubalin aurena na shekaru 40,"
"Wani lokaci ne a 2018, na zo Legas aiki daga Abuja. Kamar yadda aka saba, ina shirin kwanciyar barci da kusan karfe 3:00, sai matata ta da ni daga magagi na."
"Da farko na ji tsoro, na dauka an samu matsalar tsaro ne, amma sai yanayinta ya saba yiwuwar hakan, ta kasance a natse."

- Lai Mohammed

Kara karanta wannan

Ramadan: Dan takarar shugaban kasa na LP ya ziyarci Musulmi an yi buda baki da shi

An yada cewa Lai yana da $1.3bn

Leadership ta rahoto Lai yana cewa daga nan sai matarsa ta fada masa akwai muhimmin batun da ta ke so su tattauna a kai.

Kwatsam uwargidar ta bijiro masa da rade-radin cewa yana da hannu a wani asusun kasar waje da yake dauke da Dala biliyan 1.3.

Lai yake cewa bai taba tunanin sahibarsa za ta yarda da labaran karya da ake yawa a kan gwamnatin Muhammadu Buhari ba.

A nan ya shafe awanni biyu cikin gumi, yana so ya nunawa matarsa gaskiyar lamarin.

Ya tsohon Minista ya wanke kan shi?

Tsohon kakakin APC na kasa ya dauka na’urar lissafi, ya nunawa matarsa adadin kudin da gwamnatin tarayya ta yi kasafi tun 2015.

A karshe ya yi mata bayani cewa abin da ake warewa ma’aikatarsa bai taba wuce N5bn, a wancan lokacin kuwa bai zarce $12.5m.

Kara karanta wannan

Da gaske ne Aisha Buhari ta ce tsohon Shugaban Kasa Buhari ya rasu a 2017? Ga gaskiya

Lai ya kare gwamnati daga zargi

Kafin ya bar ofis aka rahoto Lai Mohammed ya ce tun a 2015, gwamnatin APC ba ta yin katsalandan da shiga sharo-babu shanu.

Lai ya ce babu dalilin da zai sa gwamnati ta tsoma baki a kan sha’anin INEC wanda ta ke da alhakin gudanar da zabe a fadin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel