Na dawo saboda Buhari ya aminta da ni - Lai Mohammed

Na dawo saboda Buhari ya aminta da ni - Lai Mohammed

A ranar Laraba 21 ga watan Agusta, ministan labarai da ala'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya yi karin haske dangane da dalilai da suka sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada shi ministan ma'aikatar da ya rika a zango na farko.

Ya ce an sake dawo da shi a matsayin ministan labarai da al'adu a sanadiyar mafi kololuwar yarda da kuma aminci da shugaban kasa Buhari ya ke da ita a kansa.

A kalamansa ya ce "muna yiwa Allah Madaukakin Sarki godiya da ya sake ba da ikon nada ni ministan wannan ma'aikata."

Ina kuma kara yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya da ya azurta mu da tsawon rai har ya kawo mu yanzu. A daidai wannan gaba ta lokacin da muke cikinsa a yanzu ina yiwa sabbin daraktocin wannan ma'aikata lale maraba."

"Shugaban kasa ya sake zabe na a matsayin ministan gwamnatinsa saboda aminci da kuma yarda da ya shimfida a kaina. Saboda haka dole ne mu kara jajircewa wajen sauke nauyin da rataya a wuyanmu."

KARANTA KUMA: Takaitaccen tarihin ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami SAN

A ranar Larabar ne shugaban kasa Buhari ya rantsar da majalisar minictocinsa, domin fara aiki gada-gadan a wa'adi na biyu na mulkinsa bayan lashe babban zaben kasa da aka gudanar a watan Fabrairu.

A watan Yulin da ya gabata ne majalisar dattawan kasar ta tantance tare da bayar da sahalewarta a kan sabbin ministoci 43 da shugaban kasar ya gabatar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel