Buhari ya aika da takardar kasafin kudin shekarar 2017

Buhari ya aika da takardar kasafin kudin shekarar 2017

A jiya ne aka samu labarin cewa har Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da takardun kasafin kudin 2017 Majalisa

Shugaban Kasar, Muhammadu Buhari ya aika da takardar zuwa majalisar dattawa

Sai majalisa ta amince da takardar sannan za a karbi asalin kudin kasafin shekara mai zuwa

Buhari ya aika da takardar kasafin kudin shekarar 2017

 

 

 

Reuters ta rahoto cewa har Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya fara aikawa da takardun kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2017 zuwa Majalisar Dattawa ta Kasar. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika takardar da za a duba kasafin kudin shekara mai zuwan ne domin a amince.

Wannan takarda tana dauke da yadda Najeriya za ta kashe kudin ta shekara mai zuwa, har sai majalisar dattawar Kasar ta amince sannan za a kawo ainihin kundin kasafin kudin shekara mai zuwan ta 2017.

KU KARANTA: An sace wasu kudi $17bn lokacin Jonathan

Takardar ta nuna cewa Najeriya za ta kashe Fiye da Tiriliyan shida da biliyan dari takwas, 6.86tr watau dala biliyan $22.57 a shekara mai zuwa. Wannan kudi dai ya ma fi na bana da aka lissafa Tiriliyan 6.06. Najeriya dai ba ta taba kasafin irin wannan makudan kudin ba a tarihi.

Tattalin arziki Najeriya dai ya ruguje bayan karyewar darajar mai a duniya, haka kuma Kasar ba fama da tsagerun Neja-Delta wanda suke fasa butatan man kasar, don haka gangan man da kasar ta ke fitarwa sun ragu sosai. An dai kiyasta gangar mai a kan $42.5 a kasafin na 2017, da kuma $1 a kan N300.2500.

Asali: Legit.ng

Online view pixel