Gwamnatin Bola Tinubu Ta Gurfanar da Shugaban Kungiyar Fulani Ta Miyetti Allah, Bodejo

Gwamnatin Bola Tinubu Ta Gurfanar da Shugaban Kungiyar Fulani Ta Miyetti Allah, Bodejo

  • Gwamnatin shugaba Tinubu ta maka shugaban kungiyar Miyetti Allah a kotu bisa zargin kafa kungiyar ta'addanci
  • Bello Bodejo ya musanta zargin da ake masa, ya bayyana gaskiyar dalilin da yasa ya kafa kungiyar ta 'yan banga
  • Rahoto ya nuna yadda aka Bello a watan Janairu a daidai lokacin da yake kaddamar da kungiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - An gurfanar da Bello Bodejo daya daga shuganannin kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zarginsa da kafa kungiyar masu aikata ta'asa ba bisa ka’ida ba.

An gurfanar da Bodejo ne a ranar Juma’a kan tuhume-tuhume uku da ofishin AGF ya shigar, inda ake tuhumarsa da karya dokar yaki da ta’addanci ta shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Zargin cushe a kasafi: Tinubu ya dira kan Sanata Ningi, ya kwance masa zani a kasuwa

An gurfanar da shugaban Fulani a kotu kan zargin ta'addanci
Kafa kungiyar 'yan banga ta sa an gurfanar da shugaban Fulani | Hoto: @officialABAT, @therleez
Asali: Twitter

Sai dai, Bodejo ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi a gaban alkali, daga nan ne mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun hukumar leken asiri ta DIA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda batun ya samo asali

Mai shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar 27 ga watan Mayu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

An kama Bodejo ne a ranar 23 ga watan Janairu a ofishin Miyetti Allah da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa a yayin kaddamar da wata kungiyar ‘yan banga.

Kungiyar al’adun Fulanin ta kaddamar da kungiyar ‘yan banga ne kwanan nan a Nasarawa da zimmar samarwa makiyaya kariya daga dukiyarsu da rayukansu, rahoton The Cable.

Meye yasa aka kafa kungiyar?

Kara karanta wannan

Kano: Sabuwar takaddama ta taso yayin da 'yan sanda suka bukaci diyya daga Murja Kunya

Bodejo ya ce kungiyar ‘yan bangar an kafa ta ne don ta taimakawa jami’an tsaro wajen yaki da miyagun laifuka a jihar ta Arewa ta Tsakiya.

Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin tsare Bodejo na tsa kwanaki 15 a hannun hukumar leken asiri ta kasa NIA tun farko.

Bayan karewar wa’adin, alkalin kotun tarayya Inyang Ekwo, ya kara wa’adin kwanaki bakwai a ci gaba da tsare shugaban.

Bello Bodejo ya maka gwamnatin Tinubu a kotu

A nasa bangaren, Bello Bodejo, ya shigar da gwamnati kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Daily Trust ta ruwaito Bello Bodejo na neman kotun ta ba da umarnin a sake shi ba tare da wani sharadi ba daga hannun hukumar leken asiri ta kasa.

Lauyan Bodejo, Mohammed Sheriff, ya shaida wa kotun cewa, sun gabatar da bukatar ne bisa dogaro tauye 'yancinsa da hukumar ta yi na kin sakinsa gabanin zuwa kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel