Abin da Majalisar Dattawa Ta Buƙaci Tinubu Ya Yi Wa Iyalan Sojojin da Aka Kashe a Delta

Abin da Majalisar Dattawa Ta Buƙaci Tinubu Ya Yi Wa Iyalan Sojojin da Aka Kashe a Delta

  • Majalisar dattawa ta buƙaci gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu da ta biya diyya ga iyalan sojojin da aka kashe a jihar Delta
  • Haka zalika, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar an kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika, domin a hukunta su
  • Kwanaki bayan kisan, hedikwatar tsaro ta ce jami’ai 17 da suka hada da kwamandan bataliya ta 181, da wasu manyan sojoji biyu, da kaftin daya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan diyya ga iyalan sojoji 17 da aka kashe.

An gabatar da bukatar ne a zaman da majalisar tayi a ranar Talata, yayin da sanatocin suka yi shiru na minti daya domin karrama sojojin da suka rasa rayukansu a Okuama da ke jihar Delta.

Kara karanta wannan

Badaƙalar $300m: Majalisa ta ba ministan Tinubu sa'o'i 72 ya gurfana gabanta, sun samu bayanai

Majalisa ta bukaci diyyar sojojin da aka kashe a Delta
Majalisar dattawa ta buƙaci gwamnati ta biya diyyar sojojin da aka kashe a Delta. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

A yayin zaman, an gabatar da kudiri mai muhimmanci na kan kashe jami'an sojin Najeriya da kuma wajabcin gudanar da bincike cikin gaggawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ya ruwaito cewa shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojojin Najeriya, Sanata Abdulaziz Yar’adua ne ya gabatar da kudurin.

Bukatun majalisar dattawa ga Tinubu

Daga nan kuma aka ba da umarni ga kwamitocin sojojin kasa da na ruwa da na tsaro da su hada kai da hukumar sojin Najeriya domin gudanar da bincike kan lamarin.

An kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar an kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika, domin a hukunta su kan abun da suka aikata.

Kwanaki bayan kisan, hedikwatar tsaro ta ce jami’ai 17 da suka hada da kwamandan bataliya ta 181, da wasu manyan sojoji biyu, da kyaftin daya, da kuma jami’an bataliyar 12 na daga cikin wadanda aka kashe.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 16: Majalisar dattawa ta dauki muhimmin mataki

Jerin sunayen sojojin da aka kashe

Hedikwatar tsaron ta bayyana sunayen wadanda aka kashe kamar haka, kamar yadda shafin BusinessDay ya ruwaito:

Lt Col AH Ali, kwamandan bataliya ta 181 'Amphibious Battalion'

Maj SD Shafa (N/13976)

Maj DE Obi (N/14395)

Capt U Zakari (N/16348)

SSgt Yahaya Saidu (#3NA/36/2974)

Cpl Yahaya Danbaba (1ONA/65/7274)

Col Kabiru Bashir (11NA/66/9853)

LCol Bulus Haruna (16NA/TS/5844)

Lal Sole Opeyemi (17NA/760719)

LCpl Bello Anas (17NA/76/290)

LCpl Hamman Peter (NA/T82653)

LCpl Ibrahim Abdullahi (18NA/77/1191)

Pte Alhaji Isah (17NA/76/6079)

Pte Clement Francis (19NA/78/0911)

Pte Abubakar Ali (19NA/78/2162)

Pte Ibrahim Adamu (19NA/78/6079), da kuma

Pte Adamu Ibrahim (21NA/80/4795).

Okuama: Su wa ke da alhakin kashe sojoji?

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi zargin cewa wasu 'yan bindiga ne suka shigo ƙasar suka kashe sojoji 17 a jihar Delta.

Akpabio wanda ya bayyana hakan a zaman majalisar na yau Talata, ya ce ba ya tunanin mutanen yankin Neja Delta ne suka aikata kisan kamar yadda wasu ke tunani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel