Zazzabin Cizon Sauro: Gagara Badau!
- Masana sun yi bayanin abun da ya sa yaki da zazzabin cizon sauro ya ke gagara
- An dade a na fama da cutar kuma tun lokaci mai tsawo a ke fafutukar kawar da ita
- Sai dai hakan ya faskara don matsaloli da kuma cikas da yaki da cutar ke fuskanta
Kowa ya san yadda zazzabin cizon sauro ya addabi al'ummar Najeriya da kuma yadda a ke ta fafutukar magance shi tun lokaci mai tsawo. Sai dai kuma kash, kusan lamarin jiya iya yau ne. Don kuwa wadanda su ka yi fama da cutar a sherar 2016 sun kere na 2015.
Duk da dai an samu saukin yawaitar cutar a wannan shekara, amma bambancin ba wani abun ku zo ku gani bane. Toh wai shin menene matsatar? Tambayar ce ta sa wani mai suna Oyeyemi Gbenga-Mustapha ya tattaro bayanai don wayar da kan jama'a.
An samu bayanai daga Kungiyar Kiwon Lafiya na Duniya (WHO) cewan rashin wadataccen maganin sha da ragan sauro da kuma maganin kwari da na sauro, su na haifar da yawaitan kamuwa da cutar, sannan su na kawo cikas ga yaki da cutar.
DUBA WANNAN: Wani dan sanda yayi makil da giya ya harbe wani mutum har lahira
A kasashe kuwa irin Najeriya, baya ga rashin maganin, mafi yawan wadanda su ka samu, jabu ne. Jabun magani kuwa koda ya yi tasiri, to na dan wani lokaci ne. Wani jabun magani ma dauke ya ke da kwayoyin cutar da zai haifar da wata cutar ta daban.
Don haka ne wani jami'in Hukumar NAFDAC, da ya nemi a sakaya sunan sa, ya yi kira ga jama'a da su kiyaye kuma su taimaka wurin yaki da kawar da jabun magani da su ke yawo a kasuwanni.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng