Halin Kunci: Kwastam Ta Ziyarci Buhari, Sun Yi Magana Kan Bude Iyakoki da Tinubu Ke Shirin Yi

Halin Kunci: Kwastam Ta Ziyarci Buhari, Sun Yi Magana Kan Bude Iyakoki da Tinubu Ke Shirin Yi

  • Yayin da kwanturolan hukumar Kwastam ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi magana kan bude iyaka
  • Mista Adewale Adeniyi ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ne yake da ikon bude iyakokin kuma yanzu haka ana tattaunawa a kai
  • Adeniyi ya bayyana haka ne a jiya Asabar 9 ga watan Maris yayin ziyara ga Buhari da kuma garin Kongolam da ke karamar hukumar Mai’adua

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina – Kwanturolan hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi ya ce Shugaba Tinubu ne kadai ke da damar bude iyakar Najeriya.

Adeniyi ya bayyana haka ne a jiya Asabar 9 ga watan Maris a garin Kongolam, a karamar hukumar Mai’adua da ke jihar Katsina, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Kiran juyin mulki: Minista ya dauki zafi, ya bada umarni ga jami'an tsaro a dauki mataki

Kwastam ta yi bayanin shirin bude iyaka da Tinubu ke yi a yanzu
Hukumar Kwastam ta ce Tinubu na kokarin bude iyakar da Buhari ya rufe. Hoto: Bola Tinubu, Adewale Adeniyi, Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Shirin da Tinubu ke yi domin bude iyaka

Kwanturolan ya kuma ziyarci tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya ba shi tabbacin samar da sauki ga ‘yan kasuwa a kan hanyoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adewale ya ce suna kokarin saka ido kan ‘yan kasuwar da ke kokarin fitar da kayan abinci waje domin tabbatar da an yi amfani da abincin a iya Najeriya.

Yayin da ake ta kiran Shugaba Tinubu ya yi kokarin bude iyakokin kasar ko za a samu saukin rayuwa, Adewale ya bayyana tsare-tsaren da suke yi.

Ya ce a yanzu haka ana ci gaba da ganawa da masu ruwa da tsaki kan yiwuwar bude iyakokin kasar.

“Da zarar ganawar tazo karshe kan bude iyakokin, za a dauki mataki kan lamarin ba tare da bata lokaci ba.

- Adewale Adeniyi

Kara karanta wannan

Ka kula da lafiyarka madadin yawace yawace, Malamin addini ya ba Tinubu shawara

Adewale har ila yau, ya bukaci jami’ansu da su tabbatar sun kakkabe duk wata matsala da za ta kawo cikas a harkokin kasuwanci, Pulse ta tattaro.

Wasu tsare-tsare aka bi domin dakile tsadar abinci?

Wannan na zuwa ne yayin da kwanturolan ya bayyana wasu matakai da suke dauka domin dakile yawan tsayar da motoci a wuraren binciken ababan hawa.

Ya ce hakan zai taimaka wurin tabbatar da harkokin kasuwanci sun gudana ba tare da matsala ba inda ya ce sun yi hadaka da ‘yan kasuwa kan haka.

“Muna sane da irin korafin wadanda ke kusa da iyakoki musamman yawan wuraren binciken ababan hawa ke yi da kuma rufe iyakokin.”
“Mun gabatar da korafe-korafe ga Shugaba Tinubu wanda ya ke sauraran korafin mutane, ya umarci mayar da kayan abincin da muka kama ga masu shi idan har za a siyar a kasuwanni.”

- Adewale Adeniyi

Kwastam za ta sake raba abinci

Kara karanta wannan

Ban taba ganin irinsa ba, Hadimin Tinubu ya fadi lokacin da Tinubu ke kwanciya duk daren Allah

Kun ji cewa hukumar Kwastam ta yi alkawarin sake siyar da kayan abinci da ta kama karo na biyu bayan cafke tirela makare da abinci a bakin iyaka.

Hukumar ta na raba kayan abincin ne ga ‘yan kasar a farashi mai rahusa yayin da take kokarin dakile fitar da abinci wajen kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel