Duk da Halin Kunci, Kwastam Ta Sake Cafke Tirela Makare da Kayan Abinci Zuwa Ketare

Duk da Halin Kunci, Kwastam Ta Sake Cafke Tirela Makare da Kayan Abinci Zuwa Ketare

  • Yayin da ake cikin matsin rayuwa a Najeriya, hukumar Kwastam ta sake cafke wata tirela makare da wake zuwa kasar waje
  • Hukumar ta yi nasarar cafke motar a bakin iyakar Seme da ke makare da buhunan wake har 400 domin tsallakawa da su waje
  • Legit Hausa ta tattauna da malami kuma masanin tattalin arziki kan lamarin rabon abincin da Hukumar ke shirin yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas – Hukumar Kwastam ta cafke tirela makare da wake a bakin iyakar Najeriya domin fitar da shi ba bisa ka’ida ba.

Hukumar ta kama kayan abincin ne a motar da ke dauke da buhunan wake fiye da 400 da kudinsu ya kai naira miliyan 61.

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa ya fadi tsawon lokacin da za a dauka kafin fita daga matsala

Kwastam ta dakile wata babbar mota makare da buhunan kayan abinci
Hukumar ta sanar da cewa za ta sake raba kayan kayan abincin ga jama'a. Hoto: @CustomsNG.
Asali: Twitter

Wane mataki hukumar za ta dauka kan abincin?

Kwanturolan hukumar a yankin, Timi Bomodi shi ya bayyana haka a jiya Talata 5 ga watan Maris a ofishin hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, hukumar ta ce za ta rarraba kayan da ta kama yayin da ake cikin wani irin matsi na tsadar rayuwa.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta kame kayayyakin abinci wanda suka rinka siyar wa ga jama’a cikin farashi ma rahuwa.

Martanin hukumar Kwastam kan kayan abincin

"Duba da yadda muke cikin matsin tattain arziki da karancin kayan abinci da kuma hana fitar da abinci ba bisa ka'ida ba, mun kama buhanan wake 400 makare a babbar mota.
"Mun ajiye kayan a ma'ajiyar gwamnati domin adana su da kuma raba kayan a nan gaba."

- Timi Bomidi

Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta siyar da shinkafa da ta kwace ga jama'a cikin farashi mai rahuwa a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Jerin wasu jihohin Arewacin Najeriya da ke da Hukumar Hisbah

Legit Hausa ta tattauna da malami kuma masanin tattalin arziki kan lamarin rabon abincin

Masanin tattalin arziki, Bello Lamido ya ce kwata-kwata ba ya goyon bayan tsarin rabon abinci.

"Babu wani sauyi da wannan zai kawo ga hauhawar farashi, madadin wannan gwara a samar da kayan noma na zamani da tallafin kudi da kuma bude wa manoma kasuwa idan sun yi nomansu."

Lamido Bello

Kwastam za ta sake rabon abinci

Kun ji cewa Hukumar Kwastma za ta sake rabon abinci karo na biyu bayan kwace kayan abinci da ake shirin fita da su ba bisa ka'ida ba.

Ofishin hukumar da ke shiyyar Oyo da Ogun shi ya bayyana haka inda ya ce zai bi dukkan tsarin da ya dace.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta siyar da shinakafar da ta kama a Legas da ya jawo rasa rayuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel