Tsadar Siminti: Majalisa Za Tayi Ganawa Ta Musamman da Dangote, BUA da Sauransu

Tsadar Siminti: Majalisa Za Tayi Ganawa Ta Musamman da Dangote, BUA da Sauransu

  • Majalisar wakilai ta gayyaci Dangote, BUA da sauran kamfanonin siminti a Najeriya don tattauna wa kan tsadar siminti a kasar nan
  • Gayyatar ta ya biyo bayan kudirin da Hon. Gaza Jonathan Gbefwi, da Hon. Ademorin Kuye suka gabatar yayin zaman majalisar a Abuja
  • Gbefwi da sauran 'yan majalisu sun koka kan yadda kamfanonin suka kara kudin simintin duk da matakan da gwamnatin tarayya ta dauka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar Laraba ne majalisar wakilai ta gayyaci Dangote, BUA da sauran kamfanonin siminti a Najeriya bisa zargin karin farashin siminti da kamfanonin suka yi.

Majalisar ta kuma umarci kwamitocinta masu kula da daskararrun ma’adanai, kasuwanci, masana’antu da ayyuka da su binciki karin farashin simintin da aka yi ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Arewa ta barke da murna bayan ware $1.3bn kan aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi

Majalisa ta nemi zama da Dangote, Bua da sauran su.
Majalisar ta koka kan yadda kamfanoni suke karin kudin siminti. Hoto: @AlikoDangote, @BUACement
Asali: Getty Images

Illolin da karin kudin siminti ya haifar

Gayyatar ya biyo bayan kudirin da Hon. Gaza Jonathan Gbefwi, da Hon. Ademorin Kuye suka gabatar yayin zaman majalisar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Vanguard ta ruwaito Hon. Gbefwi yayin gabatar da kudurin ya ce kamfanonin sarrafa simintin sun kara farashinsa da kusan rabin kudin da ya ke a baya.

Dan majalisar ya ce karin kudin ya haifar da tashin kudin gine-gine, wanda ya zama silar karin kudin hayar gidaje a kasar.

Kamfanonin siminti na fakewa da canjin kudi

Ya kuma kara da cewa, ana samun dukkan kayan hada siminti da suka hada da lime, silica, alumina, iron oxide, da gypsum a Najeriya kuma ba su da tasiri da canjin kudi.

Rahoton Leadership ya rahoto Gbefwi ya nuna damuwa kan yadda kamfanonin ke amfani da canjin kudi wajen kara farasin siminti alhalin kudin kayan sarrafa shi ba su tashi ba.

Kara karanta wannan

"Yadda Emefiele ya ba matarsa kwangilar biliyoyin Naira lokacin yana gwamnan CBN"

Shi ma da yake magana kan kudirin, Yusuf Gagdi ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta dauki matakai na kawo sauki ga kamfanonin siminti, amma duk da haka farashin ya karu.

Gwamnati ta gana da Dangote, BUA

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta gana da kamfanonin sarrafa siminti da suka hada da Dangote, BUA, Lafarge da sauransu, domin kawo karshen tashin farashin siminti a kasar.

Sai dai rahoton ta Legit Hausa ta tattara, ya nuna cewa farashin simintin na ci gaba da hauhawa a fadin kasar duk da yarjejeniyar da kamfanonin da gwamnati suka cimmawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel