Ramadan 1445: Wane Lokaci Ne Ake Gama Sahur? Fitaccen Malami Ya Ba da Amsa

Ramadan 1445: Wane Lokaci Ne Ake Gama Sahur? Fitaccen Malami Ya Ba da Amsa

  • Kasashe da dama sun sanar da fara azumin watan Ramadan, lokacin da Musulmi suka fi so musamman domin gudanar da ibada
  • Musulmi a watan Ramadan na kamewa daga cin abinci ko shan ruwa da kuma saduwa da iyali daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana
  • Ana samun yawan tambayoyi game da lokacin da za a daina yin sahur; wanda Sheikh Ahmad Kutty, ya ba da amsa tare da karin bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sahur shi ne abincin da musulmai ke ci kafin ketowar alfijir yayin daukar azumi na Ramadan ko nafila, duk da mutum na iya yin azumin ko bai ci abinci ba.

Baya ga zama sunna (abin da Annabi ya yi umarni da ayi), sahur yana bai wa mai azumi kuzari da kare shi daga kasala ko tsananin yunwar da azumi ke haifarwa.

Kara karanta wannan

Ramadan: Muhimman abubuwa 10 da suka dace Musulmi ya kauce masu a wata mai albarka

Azumin watan Ramadan 2024
Sheikh Ahmad Kutty ya yi karin haske kan lokutan fara wa da daina yin sahur. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wane lokaci ne ake gama sahur a azumi?

Ana son mai niyyar daukar azumi ya yi sahur domin a cikin sahur akwai falala da albarka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu mutane (kamar masu amfani da shafin X) sun nemi sanin lokacin da ya kamata su daina cin abinci a lokacin sahur.

Sheikh Ahmad Kutty ya ba da amsa kan azumi

Sheikh Ahmad Kutty babban malamin addinin musulunci a cibiyar musulunci ta Toronto, Ontario, Canada ya bada amsa akan wadannan tambayoyi.

Ya yi bayani cewa:

"Akwai lokuta biyu na dakatar da cin abinci yayin sahur, wato lokacin da aka fi so da lokacin da aka wajabta.
Mafificin lokacin daina cin abinci shine mintuna goma kafin lokacin fajir. Don haka idan lokacin ketowar alfijir ya kasance karfe 5:25 na safe, sai a daina cin abinci da misalin karfe 5:15."

Kara karanta wannan

Mutane miliyan 1.25 za su ci gajiyar shirin tallafin Ramadan daga hannun Sanata Yari

Kiran Sallah da daina cin abinci

Sheikh Kutty ya kara da cewa:

Sai dai lokacin da aka wajabta daina cin abinci a lokacin yin sahur na iya kai wa karfe 5:25 na safe (idan shi ne lokacin alfijir a garin da kake), bayan nan kuma ana ganin haramun ne cin abinci.
Idan kuma ladani na yin kiran Sallah a kan lokaci, to wannan shi ne zai zama lokacin daina cin abincin sahur.
Amma idan aka yi kiran Sallah alhalin akwai sauran abinci a bakin mutum, to zai iya hadiye wa, sai dai ba zai ci gaba da cin na kwanon da ke gabansa ba.

Kara karanta bayanai akan Ramadan:

Ramadan 1445: Abubuwan da ya kamata ku sani game da lokutan azumi a fadin duniya

Ramadan 2024: Jerin kasashen da Musulmai za su yi azumi mafi tsawo da gajarta

Ramadan: Muhimman abubuwa 10 da suka dace Musulmi ya kauce masu a wata mai albarka

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Sultan ya sanar da ganin watan Ramadan

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci (NSCIA) ya bayyana ganin watan Ramadan 2024 a Najeriya.

Sarkin Musulmi ya ce an ga jinjirin watan a jiya (Lahadi) don haka za a tashi da azumi a yau (Litinin) 11 ga watan Maris, 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel