Dama Ta Samu: Gwamnan APC Ya Amince da Ɗaukar Ma'aikata Sama da 1000 a jihar arewa

Dama Ta Samu: Gwamnan APC Ya Amince da Ɗaukar Ma'aikata Sama da 1000 a jihar arewa

  • Gwamnatin Jigawa karkashin Gwamna Umar Namadi za ta ɗauki ma'aikatan lafiya 1,124 domin inganta harkokin lafiya
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa, ya ce majalisar zartarwa ta amince da haka a zaman ranar Alhamis
  • Ya ce za a maida ma'aikatan lafiya na wucin gadi J-Health su zama cikakkun ma'aikata kana a ɗauki waɗanda zasu maye gurbinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da daukar ma’aikatan lafiya 1,124 da suka yi aiki a baya a matsayin ma’aikatan wucin gadi karkashin shirinta na J-Health.

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa.
Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Daukar Ma'aikatan Lafiya Sama da 1000 Hoto: Umar Namadi
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu, Alhaji Sagir Musa, ya fitar ranar Juma’a a Dutse.

Kara karanta wannan

Wasu hadimai sun yi jabun sa hannun gwamnan APC don sace kuɗi? Gaskiya ta bayyana

A cewar Musa, majalisar zartaswar jihar Jigawa ta amince da ɗaukar ma'aikatan aikin dindindin a zamanta na ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"A ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba, 2023 majalisar zartaswa ta jiha (SEC) ta amince da ɗaukar ma'aikatan lafiya 1,124 (na tsarin J-Health) su zama cikakkun ma'aikata."

Yadda za a ɗauki ma'aikatan kuma a maye gurbinsu

Musa ya ce wannan matakin ya yi daidai da kudurin gwamnatin Jigawa karkashin Gwamna Umar Namadi na inganta hanyoyin kiwon lafiya cikin sauki a fadin jihar.

Kwamishinan ya ƙara da cewa majalisar ta kuma amince da ware kudi N959.2m na albashi da alawus ga ma’aikatan lafiyan su 1,124.

Ya ce sun hada da ma’aikatan shirin J-Health 924: ma’aikatan lafiya 200, likitoci 40, masu hada magunguna 30, da ma’aikatan jinya 20.

Kara karanta wannan

Mambobi sun zaɓi sabon shugaban majalisar dokokin Jihar Nasarawa da mataimaki

A rahoton Daily Nigerian, Musa ya ci gaba da cewa:

"Domin tabbatar da ɗaukar ma'aikatan tsarin J-Healtha aiki, ma'aikatar lafiya ta jihar Jigawa zata shirya masu jarabawar gwaji."
"Bayan haka majalisar ta amince da sake ɗaukar haifaffun jihar Jigawa 1,000 waɗanda suka karanta kwasa-kwasan da suka shafi harkar lafiya a tsarin J-Health domin maye gurbin waɗanda aka ɗauka aiki."

Gwamnatin Ondo ya faɗi gaskiya kan jita-jita

A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Ondo ta yi fatali da jita-jitar cewa an haɗa jabun sa hannun Gwamna Rotimi Akeredolu wajen wawure kuɗin baitul mali.

Misis Bamidele Ademola-Olateju, kwamishinar yaɗa labarai da wayar da kai ta Ondo ce ta bayyana gaskiya ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel