Ustaz Abu Jabir PenAbdul: Me ake nufi da niyya, kuma ya ake yin niyyar azumin Ramadan?

Ustaz Abu Jabir PenAbdul: Me ake nufi da niyya, kuma ya ake yin niyyar azumin Ramadan?

- Ana sa ran a fara azumin watan Ramadan a ranar Talata ko Laraba a Najeriya

- Ustaz Abu Jabir PenAbdul ya yi bayani game da abin da ya shafi daukar niyya

- Babban Malamin ya bayyana cewa mutum ya na kudirta yin niyya ne a zuciya

Yayin da azumin watan Ramadan ya gabato, Legit.ng Hausa ta yi hira da babban malami Abu Jabir PenAbdul game da abinda ake bukatar Musulmai su sani.

Ustaz Abu Jabir PenAbdul ya yi bayani game da abin da ya shafi niyyar yin azumi, inda ya hakaito maganar shehin malamin musulunci, Imam Ibn Taiyimiyyah.

Ya ce: Muhallin niyya ya na cikin zuciya, ba furta wa ake yi ba. Mutum ya na daukar niyya a zuciyarsa cewa zai yi azumi 29 ko 30 (ya danganta da ganin wata).

KU KARANTA: An cafke Malamin da ya bugi yaro, ya nemi ya aika shi barzahu

Babban malamin ya ke cewa mutum zai kudira cewa zai yi azumin farilla ne na watan Ramadan.

Abu Jabir wanda aka fi sani da PenAbdul ya bada misali da wanda ya bar gida, ya yi alwala, ya tafi masallaci, ya ce wannan ba ya bukatar furta niyyar sallah.

Ga wanda bai samun yin niyya ba har bayan fitowar alfijir, zai dauki niyyarsa a makaren, ya cigaba da kama-baki, bayan watan Ramadan ya rama azumin ranar.

Abu Jabir PenAbdul ya ce ana yin niyyar azumin Ramadan ne kafin alfijir, sabanin azumin nafila wanda Manzon Allah SAW ya kan shirya azuminsa da rana tsaka.

Ustaz Abu Jabir PenAbdul: Me ake nufi da niyyar azumin Ramadan kuma ya ake yin ta
Ustaz Abu Jabir PenAbdul Hoto: www.legit.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Qadirawa su na so a kyale Sheikh Abduljabbar ya yi tafsirin azumi

Shehin ya bayyana cewa duk wadanda su ka bijire wa Mai alfarma Sarkin Musulmi, sun saba wa sunnah domin addinin musulunci ya ginu ne a kan hadin-kai.

Abu Jabir PenAbdul ya ce abin da ya dace shi ne mutum ya dauki azumi kuma ya sha ruwa tare da sauran al’umma kamar yadda Manzon Allah SAW ya koyar.

Malam Abu Jabir PenAbdul ya bayyana cewa Najeriya ta na la’akari ne da ganin watan ta, ya ce babu abin da ya hada lissafin kasar nan da kasar Saudi Arabia.

A ranar Lahadi ne ku ja ji labari cewa Sarkin Musulmi ya umarci al'umar Musulman kasar nan su nemi jinjirin Ramadan ranar Litinin 12 ga watan Afrilu, 2021.

Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bada wannan umarnin ne ta baki shugaban kwamitin da ke ba shi shawara a kan al'amuran addinin musulci a fadarsa a Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel