Ramadan 1445: Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Lokutan Azumi a Fadin Duniya

Ramadan 1445: Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Lokutan Azumi a Fadin Duniya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A ranar Litinin 11 ga Maris ko kuma Talata 12 ga watan Maris za a fara azumin watan Ramadan bayan an tabbatar da ganin watan a kasashen duniya.

Azumi na farawa daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana, kuma yana ɗaukar daga sa'o'i 12 zuwa 17, ya danganta da inda mutum ya ke rayuwa a duniya.

Watan Ramadan dai shi ne watan da aka saukar da ayoyin farko na Alqur’ani ga Annabi Muhammad (Allah ya kara masa yarda) fiye da shekaru 1,400 da suka gabata.

Lokutan azumin 2024 a fadin duniya
Ramadan 2024: Za a fara azumi a ranar 11 ko 12 ga watan Maris. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Islamic finder ta ruwaito cewa azumi yana tattare da kamewa daga ci, sha, shan taba da jima'i (daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana) don samun "takawa", ko neman lada daga Allah.

Kara karanta wannan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya buƙaci a fara duba jinjirin watan azumin Ramadan 1445H

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene yake jawo bambanci a lokutan fara azumi?

Za a fara azumin Ramadan da wuri a wannan shekara. Wannan ya faru ne sakamakon watannin Musulunci sun ginu ne a kan kalandar Hijiriyya masu tsawon kwanaki 29 ko 30.

Saboda shekarar 'lunar' da ta fi gajarta a kan shekarar 'solar' da kwana 11, za a gudanar da azumin Ramadan sau biyu a shekara ta 2030.

Za a fara azumin farko a ranar 5 ga Janairu 2030, sannan a fara wani azumin a ranar 26 ga Disambar 2030.

Lokaci na gaba da Ramadan zai fara bayan 12 ga Maris zai kasance shekaru 33 daga yanzu, a shekara ta 2057 kenan.

Lokutan azumin 2024 a fadin duniya

Aljazeera ta ruwaito lokutan ketowar alfijir da faduwar rana yana bambanta a garuruwan da ke fadin duniya.

Musulman da ke zaune a kasashen kudancin duniya, irin su Chile ko New Zealand, za su yi azumi na kimanin sa'o'i 12 ne kawai.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar na ba da tallafin naira 100,000? An bankado shirin wasu mazambata

Yayin da Musulman da ke zaune a yankunan arewaci, kamar Iceland ko Greenland, za su yi azumi na fiye da sa'o'i 17.

A wasu kasashen arewacin duniya, irin su Longyearbyen na Norway, inda rana ba ta faɗuwa daga ranar 20 ga Afrilu zuwa 22 ga Agusta, shari'a ta ba su damar amfani da lokutan azumi a Makka, Saudiya, ko kuma ƙasar musulmi mafi kusa.

Garuruwan masu sahur da buda baki a lokaci daya

Abincin da ake ci domin fara azumi ana kiransa sahur, yayin da ake kiran abincin shan ruwa da 'buda baki', watau bayan faduwar rana kenan.

Yayin da kasashen Nuuk, Sao Paulo, Las Vegas,Dubai, Bangkok ke sahur, a lokacin ne kuma ake buda baki a Lagos, London, New York City, Tokyo da Melbourne.

Duba lokutan sahur da buda baki a jihohin Najeriya a wannan shafin.

Awannin azumi a kasashen duniya

Ga jerin matsakaicin sa'o'in azumi a kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

Awa 16

 • Nuuk, Greenlan
 • Reykjavik, Iceland

Awa 15

 • Helsinki, Finland
 • Oslo, Norway
 • Glasgow, Scotland
 • Berlin, Germany
 • Dublin, Ireland
 • Moscow, Russia
 • Amsterdam, Netherlands
 • Warsaw, Poland
 • Astana, Kazakhstan

Awa 14

 • Brussels, Belgium
 • London, UK
 • Zurich, Switzerland
 • Stockholm, Sweden
 • Bucharest, Romania
 • Sarajevo, Bosnia and Herzegovina
 • Sofia, Bulgaria
 • Rome, Italy
 • Madrid, Spain
 • Paris, France
 • Lisbon, Portugal
 • Ankara, Turkey
 • Ottawa, Canada
 • Tokyo, Japan
 • Beijing, China
 • Athens, Greece
 • New York City, US
 • Washington, DC, US
 • Los Angeles, US
 • Tunis, Tunisia
 • Algiers, Algeria
 • Tehran, Iran
 • Kabul, Afghanistan
 • New Delhi, India
 • Dhaka, Banglades
 • Rabat, Morocco
 • Damascus, Syri
 • Islamabad, Pakistan
 • Baghdad, Iraq
 • Beirut, Lebanon
 • Amman, Jordan
 • Gaza City, Palestine
 • Cairo, Egypt

Awa 13

 • Doha, Qatar
 • Dubai, UAE
 • Khartoum, Sudan
 • Riyadh, Saudi Arabia
 • Abuja, Nigeria
 • Aden, Yemen
 • Dakar, Senegal
 • Addis Ababa, Ethiopia
 • Buenos Aires, Argentina
 • Colombo, Sri Lanka
 • Kuala Lumpur, Malaysia
 • Mogadishu, Somalia
 • Ciudad del Este, Paraguay
 • Nairobi, Kenya
 • Harare, Zimbabwe
 • Jakarta, Indonesia
 • Luanda, Angola
 • Bangkok, Thailand
 • Brasilia, Brazil
 • Johannesburg, South Africa
 • Montevideo, Uruguay
 • Canberra, Australia
 • Puerto Montt, Chile
 • Christchurch, New Zealand

Kara karanta wannan

Kannywood-Nollywood: Mista Ibu da fitattun jarumai 4 da suka mutu a shekarar 2024

Gwamna zai ciyar da talakawa a Ramadan

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya sanar da kudurinsa na ciyar da al'ummar jihar abinci a watan Ramadan na 2024.

Gwamnan ya dauki matakin amfani da babban masallaci guda daya a kowacce karamar hukumar jihar domin gudanar da rabon kayan abincin a kowacce rana har azumin ya kare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel