Mutane Miliyan 1.25 Za Su Ci Gajiyar Shirin Tallafin Ramadan Daga Hannun Sanata Yari

Mutane Miliyan 1.25 Za Su Ci Gajiyar Shirin Tallafin Ramadan Daga Hannun Sanata Yari

  • Akalla ‘yan Najeriya miliyan 1.25 daga gidaje 250,000 ne za su amfana da rabon kayan abinci na Ramadan da Abdulaziz Yari zai yi
  • Za a raba kayan abinci kamar hatsi, kayan masarufi da kayan hadi na dafa abincin domin rage radadin matsin tattali a yayin azumin
  • Shirin na da nufin taimakawa iyalai marasa galihu, ba tare da la’akari da alakar siyasa ba, da kuma zummar karya farashin kayan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Zamfara - Watan Ramadan na wannan shekarar ya fara ne a ranar Litinin 11 ga watan Maris, inda za a fara shirin raba abinci da Sanata Abdulaziz Yari ya dauki nauyi.

Jaridar Leadership ta ruwaito shugaban kwamitin raba kayan, Lawal M. Liman, ya bayyana cewa shirin zai taimaka wa gidaje 250,000, kwatankwacin mutane kusan 1,250,000.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Sanata Abdul'aziz Abubakar Yari, Zamfara
Babu siyasa a rabawa mutane miliyan 1.25 kayan abinci, in ji wakilin Sanata Yari. Hoto: Senator Abdul'aziz Abubakar Yari
Asali: Facebook

Tallafin Abdulaziz Yari na da tasiri ga al'umma

Liman, wanda ya bayyana hakan a garin Talata Mafara, jihar Zamfara, ya ce jajircewar Yari na ciyar da al’ummar jihar Zamfara da Najeriya baki daya na da tasiri a wannan lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya fayyace cewa manufar shirin ita ce ba da tallafi ga magidanta 250,000 wadanda aka tabbatar suna da bukatar tallafin a wannan wata na Ramadan.

Shugaban ya ce:

“Wannan shiri ne na al’umma, duk wanda aka ga sunansa a cikin wadanda za su samu tallafin, to shugabannin al'umma ne suka ba da sunanshi da kansu.

Yari: Babu siyasa a raba kayan abinci - Liman

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa babu siyasa a rabon kayan abincin da Yari ya shirya yi da suka hada da shinkafa, wake, masara, sukari, da sauran kayan masarufi.

Kara karanta wannan

Daliban jami'a 4 sun lakadawa abokin karatunsu duka har ya mutu, ‘yan sanda sun dauki mataki

A cewar Liman:

“Wannan ba batun jam’iyya ba ne. Sanata Yari na kowa ne, idan ka bi abubuwan da ya gabata, za ka ga cewa Yari ya kasance yana kokarin inganta rayuwar mutane ne gaba daya.
"Da wannan shiri, na tabbata hatta mutanen da ba za su amfana kai tsaye ba, za su ci gajiyar hakan saboda zai iya karya farashin abinci a Zamfara."

Sakon Tinubu ga attajiran Najeriya a Ramadan

A wani labarin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga masu hannu da shuni da su tallafawa masu bukata a cikin watan Ramadan.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Tinubu, wanda ya jaddada mahimmancin taimakon masu rauni, ya ce wannan lokacin ne jama'a suka fi bukatar samun tallafi na kayan abinci.

Shugaban ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi wa kasa addu’ar samun hadin kai, zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a cikin watan Ramadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel