"Sun Ce Ba Zan Auru Ba": Saurayi Ya Auri Matar da Ta Haifi Yara 4, An Yi Biki Na Kece Raini

"Sun Ce Ba Zan Auru Ba": Saurayi Ya Auri Matar da Ta Haifi Yara 4, An Yi Biki Na Kece Raini

  • Wata matashiyar mata da ta haifi yara hudu ta cika da farin ciki lokacin da ta hadu da mijin da ke sonta tare da yaranta
  • A ranar daurin aurenta, matar ta ce mutane sun yarda cewa ba za ta sake samun masoyi ba kuma saboda yaranta
  • Wasu masu amfani da soshiyal midiya sun garzaya sashin sharhi don bada labarin yadda suka hadu da masoyansu a matsayinsu na masu 'ya'ya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata mata da ta haifi yara hudu ta sake samun farin ciki bayan wani hadadden saurayi bature ya kamu da sonta.

Mutumin ya karbi yaran nata hannu bibbiyu kamar nasa inda ya zame masu tamkar uba. Daya daga cikin bidiyoyinta ya nuno shi yana kula da yaran.

Kara karanta wannan

Budurwa ta fada tarkon son direban Bolt da ta shiga, ta yada bidiyo

Saurayi ya yi wuff da sahibarsa
Saurayi ya auri uwar yara hudu Hoto: @mrs_turner92
Asali: TikTok

Uwar yara hudu ta samu masoyi

A wani bidiyon baya-bayan nan, matar ta nuno lokacin da ita, yaranta, da sabon sahibin nata suka shiga mota zuwa wajen daurin aurensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da take zaune a mota sanye da hadaddiyar doguwar rigar amare, ta bayyana cewa mutane sun zata ba za ta sake samun masoyi ba a matsayinta na wacce ta haihu.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a kan auren matar

Sytsie...doply ta ce:

"Mijin mahaifiyata ya aureta...mu mata biyar ne."

MaZ:

"Na fadi, 'maza za su auri wanda suke so su auri wacce suke so koda kuwa kin haifi yara ko baki haifa ba!"

SAYRAAH:

"Makwabcina ya auri wata mata da yara 6 yan cikin farin ciki."

zareenhussein ta ce:

"Ga ni a wani wuri, da yara 1 babu miji ko saurayi."

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane matsorata ne, sun cancanci hukuncin kisa, Remi Tinubu ta magantu a bidiyo

Trisha rumbie:

"Yara 3 zan yi aure wata mai kamawa."

ZeeZee ta ce:

"Aminiyata na da yara 7. kowannensu na da mahaifinsa. biyun karshe tagwaye ne. Ta yi aure a watan jiya ta auri mahaifin tagwayen."

Budurwa ta kamu da son direban Bolt

A wani labarin, mun ji cewa wata matashiyar budurwa 'yar Najeriya, @jojooflele, ta bayyana cewa ta fada a tarkon son dirabn Bolt dinta.

Da take yada bidiyonta yayin da mai tasi din ke tuka ta, matashiyar ta rikice akan kyawu da zanen jikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel