“Asiri Ya Yi Masu?” Bidiyon Matashi da Ya Auri Kyawawan ‘Yan Mata 2 a Rana 1 Ya Tada Kura

“Asiri Ya Yi Masu?” Bidiyon Matashi da Ya Auri Kyawawan ‘Yan Mata 2 a Rana 1 Ya Tada Kura

  • Wani 'dan Najeriya ya zama angon mata biyu a kwanan nan bayan ya auri kyawawan mata biyu a lokaci guda
  • Wata mata da ta halarci bikin, ta yada wani bidiyo da ta dauka a wajen taron, yayin da ta nuna rashin gamsuwarta da auren mace fiye da daya
  • Bidiyon bikin ya haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiya yayin da mata suka yi tir da zaman kishi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani matashi 'dan Najeriya da ba a bayyana sunansa ba ya auri kyawawan 'yan mata biyu a lokaci guda a Abraka, jihar Delta.

@nora_empire1 ce ta yada bidiyon a TikTok, tana mai bayyana cewa lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

"Cikar buri": Budurwa ta siya katafaren gida tana da shekaru 26, ta baje kolin cikin gidan a bidiyo

Ya angwance da mata biyu
Wani mutum ya yi wuff da mata biyu a rana daya Hoto: @nora_empire1
Asali: TikTok

Sai dai kuma @nora_empire1 bata goyon bayan auren mace fiye da daya sannan ta bayyana ra'ayinta kan auren. Kalamanta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yana auren mata biyu a rana daya a jihar Delta abraka yana faruwa kai tsaye a yau idan ni ce ba zan yarda ba Allah ya kiyaye amma matan nan sun yi kokari faaa!"

A bidiyon, amaren sun tunkari mijin nasu, inda suka zauna sannan suka durkusa don ciyar da shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Martani kan auren mata 2 a rana daya

mhizmercy82 ta ce:

"Ta yaya za su raba kudin."

Silky ta ce:

"Asiri ya yi ya rike su ne ko kuma menene ooo Allah?"

Itz sarah best collection (SB) ta ce:

"Allah da ya yiwa wadannan matan biyu zai yi mani nima."

PRICELESS_LUXURYHAIR555 ta ce:

"Hatta Ubangiji da ya halicce mu zai dunga mamaki cewa mutanen nan na yin abun al'ajabi fa."

Kara karanta wannan

Kotun Abuja ta warware auren shekara 14 saboda matsalar ma'aurata

Rabiu Aliya ta ce:

"Naira 5 ma ake likawa don Allah faaa. Allah ya kiyaye ba zan iya gwada wannan ba gwanda na auri tsoho mai kudi maimakon wannan."

Matashi ya auri mata 2 a rana daya

A wani labari makamancin wannan, wani fitaccen mai watsa shirye-shirye dan kasar Ghana, Michael Houston, wanda ya sha caccaka saboda auren mata biyu a rana daya, ya kare kansa yayin da ya bayyana illar da hakan ya janyo masa.

A kwanan nan ne Houston ya auri Felicity da Khadijah a wani gagarumin biki da aka gudanar, inda hakan ya janyo masa shan caccaka a wajen mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel