"Na Shafe Shekaru 14 Ina Dakon Sonta": Kakakin Yan Sandan Gombe Ya Saki Zafafan Hotunan Aurensa

"Na Shafe Shekaru 14 Ina Dakon Sonta": Kakakin Yan Sandan Gombe Ya Saki Zafafan Hotunan Aurensa

  • Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Gombe, Mahid Abubakar, ya shiga daga ciki a ranar Asabar, 24 ga watan Fabrairu
  • Abubakar wanda ya yi wuff da sahibarsa mai suna Nafisa, ya ce tun a 2010 ya fara ganinta kuma nan take ya kamu da sonta
  • Ya ci gaba da dakon sonta har zuwa 2016 kafin ya furta mata amma wasu daga cikin danginta suka ki, sai yanzu da Allah ya yi

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Kakakin 'yan sandan jihar Gombe, Mahid Abubakar, ya angwance da kyakkyawar amaryarsa mai suna Nafisa a ranar Asabar, 24 ga watan Fabrairu.

Sai dai kuma, labarin soyayyarsu da jami'in 'dan sandan ya bayar a shafinsa na X a ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, shine babban abin da ya dauki hankalin jama'a.

Kara karanta wannan

Matar aure ta shiga damuwa yayin da mijinta ya yi gum bayan ya kama ta tana ci masa amana tun 2023

Kakakin 'yan sandan Gombe ya shiga daga ciki
“Yadda Na Shafe Tsawon Shekaru 14 Ina Jira Don Ganin Na Auri Matata” – Kakakin ‘Yan Sandan Gombe Hoto: @MaheedMuazu
Asali: Twitter

Matashin 'dan sandan ya bayyana cewa ya fara yin arba da Nafisa a 2010, sai dai kuma bai fallasa mata sirrin zuciyarsa ba saboda karancin shekarunta a wancan lokacin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in tsaron ya bayyana cewa ya ci gaba da dakon sonta har zuwa 2016, kafin ya furta mata cewar yana sonta, kuma a lokacin yana a makarantar 'yan sanda.

Wasu cikin 'dangin Nafisa sun ki ni, Abubakar

Ya ci gaba da cewa, soyayyarsu bata samu goyon bayan wasu daga cikin 'yan uwan matar tasa ba a lokacin da ya nemi aurenta, amma hakan bai sa ya hakura ba

Kakakin 'yan sandan ya ce a watan Disambar 2023, ne 'yan uwan matarsa suka neme shi, inda suka tambaye shi ko har yanzu yana son aurenta.

A cewarsa, nan take ya yarda da auren Nafisa wacce a yanzu ta zama matarsa, saboda soyayyar da suke yi wa junansu.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Wani Magidanci Ya Halaka Ɗansa, An Gano Babban Dalili

Ya rubta a shafin nasa:

"Shekaru takwas da suka wuce, na nemi auren Nafisa, matashiyar yarinya, lokacin ina makaranta. Na fara ganinta a 2010 sannan bar wa zuciyata, duba ga karancin shekarunta har zuwa 2016.
"Duk da rashin amincewar wasu daga cikin danginta da ba a bayyana ba bayan na kammala makaranta a 2018, ban hakura ba.
"Bayan yunkuri a karo da dama, daga karshe aka tambayeni a Disambar 2023 ko har yanzu ina so. Na amince da ita, saboda son da muke yiwa junanmu kuma na auri sahibata a ranar 24/02/24. Matar Mutum Kabarinsa."

Matar aure ta shiga tsaka mai wuya

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matar aure ta yi karar mijinta a wajen iyayensa saboda ya ki cewa komai tun bayan da ya kama ta tana cin amanarsa.

Bolanle Cole, wani lauya mai kare hakkin 'dan adam, wanda ya bada labarin a shafinsa na X, ya ce wani abokin harkarsa ya kama matarsa tana cin amana sannan ya ajiye abin a matsayin sirri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel