Buga Kudi: Yadda Buhari Ya Jawo Hauhawar Farashin Kaya, Ministan Tinubu Ya Magantu

Buga Kudi: Yadda Buhari Ya Jawo Hauhawar Farashin Kaya, Ministan Tinubu Ya Magantu

  • Wale Edu, ministan kudi, ya danganta matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita da kuskuren da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi
  • Ministan tattalin arzikin kasa ya zargi gwamnatin Buhari da buga kudi ba tare da lissafi ba
  • Ministan ya bayyana cewa sakamakon matakan da Buhari ya dauka ne ya jefa Najeriya a halin kunci da take ciki a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Ministan kudi da tattalin arzikin kasa, Wale Edun, ya yi gagarumin zargi kan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da tsadar kaya ya kai kololuwa a kasar.

Ministan ya bayyana cewa naira tiriliyan 22.7 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya buga ba bisa ka'ida ba daga 2015 zuwa 2023 karkashin Buhari ne ya jefa Najeriya a halin da take ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Fitaccen basarake ya tura sako ga Tinubu kan kafa hukumar kayyade farashi

Ministan Tinubu ya fadi barnar da gwamnatin Buhari ta yi
Ministan Tinubu ya fadi yadda Buhari ya haifar da tsadar kaya Hoto: Wale Edun, Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Edun, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 7 ga watan Maris, yayin wata tattaunawa da kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a wannan lokacin, an buga tiriliyoyin nairori ba tare da tabuka komai ba.

Manufofin Tinubu zai farfado da tattalin arziki, Edun

Ministan ya kara da cewa sakamakon shekaru takwas da aka kwashe ana buga kudi ba tare da riba ba shi ne ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki da kasar ke fuskanta a halin yanzu, rahoton Daily Trust.

A makonni biyu da suka shige, majalisar dattawa ta yanke shawarar bincikar naira tiriliyan 30 da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Buhari ta kashe, wanda a cewarta, almubazaranci ne.

Sai dai kuma, ya ba kwamitin tabbacin cewa manufofin tattalin arziki da gwamnatin Bola Tinubu ta fitar don magance barnar da aka yi, zai haifar da 'ya'ya masu idanu nan ba da dadewa ba.

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa ya fadi tsawon lokacin da za a dauka kafin fita daga matsala

Cewa zai farfado da abubuwa da dama ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki da kuma inganta ma'aunin jimillar karfin tattalin arzikin kasa wato GDP.

Naira ta shiga sahun kudi mara daraja

A wani labarin, mun ji cewa babban bankin Duniya ya kawo kudin Najeriya na Naira a cikin kudin da darajarsu su ka fi kowane karyewa a Afrika.

The Cable ta ce darajar Naira da kudin Angola watau Kwanza ya na karyewa sosai, sun zama abin Allah-wadai a nahiyar Afrika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel