“Gidan Da Wigwe Ya Ba Sarki”: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Gidan Da Sanusi Ya Yi Magana a Kai

“Gidan Da Wigwe Ya Ba Sarki”: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Gidan Da Sanusi Ya Yi Magana a Kai

  • Wani 'dan Najeriya ya nunawa duniya gidan da marigayi Herbert Wigwe ya bai wa Sarki Sanusi a Victoria Island
  • Basaraken wanda ya fashe da kuka, ya yi ta'aziyyar mutuwar tsohon shugaban bankin na Access sannan ya bada labarin yadda ya tallafa masa lokacin da ya rasa sarautarsa
  • Matashin, wanda ya ziyarci Sarkin a gidan, ya wallafa wani hoton gidan sannan ya tabbatar da cewar kyauta ce daga Herbert Wigwe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani 'dan Najeriya ya saki hoton hadadden gidan da marigayi Herbert Wigwe, tsohon shugaban bankin Access, ya bai wa Sarki Sanusi a Victoria Island saboda amincin da ke tsakaninsu.

Sarkin, wanda ya karaya matuka, ya yi jawabi mai tsuma zuciya don bankwana da marigayin sannan ya tuna yadda ya tsaya masa a lokacin da aka tsige shi a matsayin Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Wigwe: Hadimin marigayi ya fadi yadda ya kaucewa tsautsayin mutuwa tare da mai gidansa

Dan Najeriya ya nuna gidan da Wigwe ya ba Sanusi
Matashin ya ziyarci Sanusi a gidan da Wigwe ya ba shi Hoto: Sirjarus/X
Asali: Twitter

Matashin, wanda ya samu damar ziyartar Sarkin a gidan, ya wallafa hoton katafaren gidan a soshiyal midiya sannan ya bayyana cewa kyauta ce ta mutuntawa daga Herbert Wigwe, wanda ya rasu a kwanan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman Muhammadu Sanusi II

"Yanzun nan nake sanin cewa Herbert Wigwe ne ya samar da wannan gidan na VI da SLS da iyalinsa suka zauna a Lagas!"

Ga wallafarsa a kasa:

Kalli bidiyon Sarki Sanusi yana magana kan Herbert Wigwe a kasa:

Yadda Wigwe ya ba Sanusi II masauki

A halin da ake ciki, mun ji a baya Legit Hausa ta rahoto cewa Muhammadu Sanusi II, tsohon Sarkin Kano, a daren Laraba, 6 ga watan Maris, ya yaba wa marigayi Herbert Wigwe, tsohon shugaban bankin Access saboda karamcin da ya nuna masa.

Wigwe na cikin mutane shida da suka mutu a ranar 9 ga watan Fabrairu, 2024, bayan da wani jirgi mai saukar ungulu da suke ciki ya yi hatsari a kusa da Nipton, a birnin California, na ƙasar Amurka.

Kara karanta wannan

Tsohon sarki Sanusi ya fadi karamcin da Wigwe ya yi masa da Ganduje ya tsige shi

A jawabin da ya yi a taron masu makoki a Legas da aka shirya saboda Wigwe, Sanusi ya bayyana cewa marigayin ne ya sauki iyalinsa a lokacin da Abdullahi Ganduje ya tsige shi.

Hadimin Wigwe ya tsallake rijiya da baya

A wani labarin kuma, hadimin marigayi tsohon shugaban bankin Access ya bayyana yadda ya sha da kyar bayan rashin tafiya tare da mai gidansa.

Sola Faleye ya ce hakan ya faru ne yayin da ya yanke shawarar daukar kayayyakinsu wanda ya hana shi tafiya da mai gidansa, Herbert Wigwe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng