Tsohon Sarki Sanusi Ya Fadi Karamcin da Wigwe Ya Yi Masa Da Ganduje Ya Tsige Shi

Tsohon Sarki Sanusi Ya Fadi Karamcin da Wigwe Ya Yi Masa Da Ganduje Ya Tsige Shi

  • Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya fashe da kuka a lokacin da yake ta'aziyyar tsohon shugaban bankin Access, Herbert Wigwe da iyalansa
  • Sanusi ya yi magana ne a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, a jihar Legas yayin taron makoki na Wigwe da aka shirya
  • Wigwe tare da matarsa ​​da ɗansa, na daga cikin mutane shida da suka mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya auku a Amurka a watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Muhammadu Sanusi II, tsohon Sarkin Kano, a daren Laraba, 6 ga watan Maris, ya yaba wa marigayi Herbert Wigwe, tsohon shugaban bankin Access saboda karamcin da ya nuna masa.

Kara karanta wannan

Saboda mace: Malamin addini ya salwantar da ran na gaba da shi a kan sabani

Wigwe na cikin mutane shida da suka mutu a ranar 9 ga watan Fabrairu, 2024, bayan da wani jirgi mai saukar ungulu da suke ciki ya yi hatsari a kusa da Nipton, a birnin California, na ƙasar Amurka.

Sanusi ya yaba wa Herbert Wigwe
Wigwe da Sanusi suna alaka mai kyau Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Totori Master
Asali: Facebook

Wane karamci Wigwe ya yi wa Sanusi II?

A jawabin da ya yi wa taron masu makoki a Legas da aka shirya saboda Wigwe, Sanusi ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dukkanmu mun ji labarinsa, game da amincinsa. Lokacin da na samu matsala a Kano, na kira shi kamar wata shida kafin a ce in bar Kano. Sai na ce masa, ‘Herbert, na san ka yi iya ƙoƙarinka don ka magance wannan matsalar, amma na tabbata cewa abin da zai faru ke nan.
"Sai ya ce mani, 'Mai martaba, ka da ka damu'. 'Duk abin da ya faru, ka da ka damu, muna tare da kai'.

Kara karanta wannan

Ana ba tsaro a kasa, Akpabio ya fito ya fadi ci gaban da Tinubu ya kawo a bangaren

"A ranar da na ji a rediyo an sauke ni, a daren jiya na san abin zai faru. Kuma na kira shi, 'Ina so in zo Legas idan abin ya faru'.
"An bayar da sanarwar da misalin ƙarfe 9:00 na safe, zuwa tsakar rana har Herbert ya kawo jirgi a Kano.
"Na sanya iyalina a cikin jirgin, babu saƙo, babu kiran waya, babu komai. Kawai na sanya su a cikin wannan jirgin na aika su Legas.
"Herbert ya tarbe su, ya ajiye su a otal, daga baya, ya samar musu gida, ya samar masu masauki.
"Zan iya ci gaba. Shola Faleye (mataimaki na musamman na Wigwe) yana nan. Herbert ya ce da ni, ‘mai martaba, idan kana son tafiya, kawai ka fada wa Shola, ina da jirgin sama. Har sai da ta kai mutane suka yi tunanin na mallaki jirgin.
"Ya ba ni motoci da direbobi, sun ba ni tsaro, sun ba ni jirgin sama, kuma ba su neman komai, kuma ba su magana a kai.

Kara karanta wannan

"Gidan da Wigwe ya ba Sarki": 'Dan Najeriya ya baje kolin gidan da Sanusi ya yi magana a kai

"Na yi shekara huɗu a Legas. Gidan da iyalina ke zaune a ciki Herbert ne ya samar da shi. Ya kasance koyaushe yana kyautatawa mutane bai damu da kansa ba."

- Muhammadu Sanusi II

Ku kalli bidiyon a nan wanda News Central Tv ya sanya:

Okonjo-Iweala ta yi ta'aziyyar Wigwe

A baya rahoto ya zo cewa shugabar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala ta yi ta'aziyyar marigayi Herbert Wigwe.

Ngozi ta bayyana rasuwar tsohon shugaban na bankin Access a matsayin babban rashi ga iyalansa da Najeriya baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel