“Cikar Buri”: Budurwa Ta Siya Katafaren Gida Tana da Shekaru 26, Ta Baje Kolin Cikin Gidan a Bidiyo

“Cikar Buri”: Budurwa Ta Siya Katafaren Gida Tana da Shekaru 26, Ta Baje Kolin Cikin Gidan a Bidiyo

  • Wata matashiyar budurwa a TikTok ta yi nasarar siyawa kanta gida, sannan ta yada wani bidiyo a soshiyal midiya domin murnar gagarumar nasarar da ta samu
  • Matashiyar, Cyndi, ta bayyana a bidiyon cewa ta siya hadadden gidan ne tana da shekaru 26 kacal a duniya
  • Haka kuma, matashiyar budurwar ta nanata cewar da guminta ta siya gidan ba wai wani ne ya siya mata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata matashiyar budurwa ta zama mai gidan kanta a yanzu, kuma ta garzaya dandalin soshiyal midiya don yin murnar wannan babbar nasara.

Matashiyar mai suna Cyndi a TikTok, ta wallafa wani bidiyo don sanar da mabiyanta cewa ta yi nasarar mallakar katafaren gida.

Kara karanta wannan

Kotun Abuja ta warware auren shekara 14 saboda matsalar ma'aurata

Matashiya ta siya katafaren gida
Ta siya gidan ne tana da shekaru 26 Hoto: TikTok/@cyndi_24.
Asali: TikTok

Abin da ya fi komai ban sha'awa shine ta siya gidan ne tana 'yar matashiyar budurwa, sannan ta biya da kudin aljihunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cyndi ta bayyana cewa shekarunta 26 kacal a duniya, wanda hakan ya sanya ta zama mai gidan kanta a ganiyar kuruciya.

Ta rubuta:

"Yanzun nan ka siya gidan da kake mafarki da kudinta a shekaru 26. Da ikon Allah ne kawai."

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a yayin da budurwa ta siya gida

@stargirl101 ta ce:

"Abun burgewa. Shin a Landan gidan nan yake?"

@TIEYA-MAI ta yi martani:

"Na taya ki murna!! Yi bayani ta yaya don Allah."

@NIKKIE ta yi martani:

'"Kada ki ji kunya. Fada mana wani aiki ya kamata mu yi muma."

@ORLANE KRYSTINA ta ce:

"Na taya ki murna, wannan babban cikar buri ne!!"

@nnequinn ta ce:

"Zan siya gidana na farko ina da shekaru 26. Amin."

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta nemi a kame dan fafutukar raba Najeriya gida biyu

Budurwa ta saki hoton gidan miliyan 1.5

A wani labarin, wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta wallafa hotunan wani katafaren gida a Twitter sannan ta ce kudin da za a siyar da shi naira miliyan 1.5.

Matashiyar, @shalomdfirst, ta haddasa cece-kuce da wannan ikirari nata, yayin da mutane da dama suka ki yarda da maganarta.

An kammala ginin gidan tsaf, kuma ta ce naira miliyan 1.5 ake so a siyar da shi, wanda mutane suka ce ya yi arha fiye da kima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel