“Oma, Ki Yafe Mun” Dan Najeriya Ya Fito Fili Ya Ba Matarsa Hakuri Bayan Ya Dirkawa Budurwarsa Ciki

“Oma, Ki Yafe Mun” Dan Najeriya Ya Fito Fili Ya Ba Matarsa Hakuri Bayan Ya Dirkawa Budurwarsa Ciki

  • A wata wallafa da ya yi a shafin Facebook, wani dan Najeriya ya amayar da abin da ke cikinsa yayin da ya ke neman afuwar matarsa
  • Mutumin mai yar biyu ya nuna nadamarsa kan yadda ya dirkawa wata budurwarsa ciki, inda ya fadi dalilin da ya sa ya aikata hakan
  • Ya kuma fadi yadda rayuwarsa ta shiga kunci tsawon shekaru biyar na aurensa saboda rashin samun haihuwa da wuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wani dan Najeriya mai suna Mubarak Abuche Musa, ya roki afuwar matarsa mai suna Oma a shafin Facebook bayan da ya dirkawa budurwarsa ciki.

A wallafar da ya yi a Facebook a ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, Mubarak ya hada da hoton matarsa tare da yin dogon bayani ya na ba ta hakuri.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Saurayi ya kashe budurwarsa bayan ta nemi ya biya ta kudin gamsar da shi

Mubarak Abuche Musa ya roki afuwar matarsa
Wani dan Najeriya mai suna Mubarak Abuche Musa, ya roki afuwar matarsa bayan da ya dirkawa budurwarsa ciki. Hoto: Mubarak Abuche Musa
Asali: Facebook

Mubarak ya fadi abin da ya sa ya kulla alakar aure da budurwarsa

Mubarak Musa ya ce ya sha suka da duk wani nauyin wulakanci tsawon shekaru biyar da matarsa saboda rashin samun haihuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce abokansa, 'yan uwansa da wasu na gulmarsa, wasu ma har a gabana suna yi, inda suke zarginsa da yin amfani da mazakutarsa wajen ayyukan tsafi.

Mubarak ya ce dukka wadannan zarge-zargen sun jefa shi cikin damuwa da neman haihuwa ko ta halin kaka, lamarin da ya sa ya fara alaka da wata matar daban.

Mubarak ya nemi yafiyar Oma

Ya nuni da cewa matarsa yanzu na da yara inda Allah ya albarkaci aurenu da mace da namiji, Mubarak ya ce ya gaza wa matarsa wacce ya bayyana ta matsayin jarumar mace.

Mahaifin 'yaya uku yanzu ya nemi afuwar matar tasa inda ya ce "dan Adam ajizi ne", tare da shan alwashin kaurace wa duk wani abu da zai kawo sabani a tsakanin su.

Kara karanta wannan

"Na rasa abokai da yawa saboda auren": Matashi ya yi wuff da tsala-tsalan yan mata 2 a rana 1

Kyakkyawar budurwa ta fashe da kuka bayan samun kyautar N20k

A wani labarin, wata kyakykyawar daliba ta fashe da kuka a lokacin da wani bakon matashi ya ba ta kyautar naira dubu 20 domin ta biya kudin makaranta.

Kafin matashin ya ba ta kudin, Saubirin ta yi magana game da abubuwan da take so ta yi a rayuwata idan ta sami dama, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel