Okonjo-Iweala, Atiku Sun Yi Martani Bayan An Tabbatar da Mutuwar Herbert Wigwe, Matarsa da Dansa

Okonjo-Iweala, Atiku Sun Yi Martani Bayan An Tabbatar da Mutuwar Herbert Wigwe, Matarsa da Dansa

  • Wani jirgin sama mai saukar ungulu ɗauke da shugaban bankin Access da Access Holdings, Herbert Wigwe da wasu mutane ya yi hatsari a jihar California ta Amurka
  • Jirgin mai suna Eurocopter EC 130, yana kan hanyarsa ta zuwa Las Vegas lokacin da abin baƙin cikin ya faru a tsakanin Nevada da California
  • Bayan hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka (FAA), ta tabbatar da cewa dukkanin mutanen da ke cikin jirgin sun mutu, Ngozi Okonjo-Iweala, ita ma ta tabbatar da rasuwar Herbert Wigwe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

California, Amurka - Shugabar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta tabbatar da rasuwar shugaban bankin Access, Herbert Wigwe.

Wigwe, mai shekara 57, matarsa, da ɗansa suna cikin fasinjoji shida a cikin wani jirgi mai saukar ungulu da ya yi hatsari a Amurka a ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

"Rayuwa babbar kyauta ce": Sakon karshe da shugaban bankin Access ya saki kafin hatsarin jirgi

An tabbatar da mutuwar Herbert Wigwe
Okonjo-Iweala, Atiku sun yi ta'aziyyar Herbert Wigwe Hoto: @HerbertOWigwe
Asali: Twitter

An tattaro cewa jirgin N130CZ da ya yi hatsarin na kamfanin Orbic Air LLC, ya taso ne daga Palm Springs, California, cikin dare amma an yi masa ganin ƙarshe a kusa da Fort Irwin/Barstow.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin Access na Wigwe na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kuɗi na Afirka.

Atiku da Okonjo-Iweala sun yi ta'aziyya

A cikin wani sakon da ta wallafa a shafinta na X ranar Asabar da daddare, 10 ga watan Fabrairu, Okonjo-Iweala ta rubuta cewa:

"Na yi matuƙar baƙin ciki da labarin mummunan rashin Herbert Wigwe, shugaban bankin Access @HerbertOWigwe da matarsa ​​da ɗansa da kuma Bimbo Ogunbanjo a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu.
"Ina miƙa ta'aziyyata ga iyalan Wigwe, Iyalin Ogunbanjo, ma'aikata da shugabannin bankin Access @myaccessbank da kuma ƙanina kuma abokin Herbert, Aigboje Aig-Imoukhuede. Allah ya sa rayukan waɗanda suka rasun su huta lafiya."

Kara karanta wannan

Herbert Wigwe: Abubuwan sani 7 game da shugaban bankin Access da ya mutu a hatsarin jirgi

Hakazalika, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓukan 2019 da 2023, yayi tsokaci kan rasuwar a shafinsa na X.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya rubuta cewa:

"Na yi matuƙar bakin ciki da jin labarin abin da ya faru wanda ya kai ga rasa Herbert Wigwe, shugaban kamfanin Access Holdings Plc, da iyalansa. Haƙiƙa Herbert Wigwe, ma’aikacin banki, mai tallata ilimi, kuma mai taimakon jama’a, ya cimma lokacinsa.
"A madadin iyalaina, ina miƙa ta'aziyya ga iyalansa da duk wanda wannan mummunan lamari ya shafa, Allah ya sa sun huta."

Saƙon Herbert Wigwe Kafin Mutuwarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban bankin Access, Herbert Wigwe, kafin mutuwarsa ya aike da saƙo mai muhimmanci.

Marigayin ya rubuta cewa rayuwar babbar kyauta ce inda ya buƙaci jama'a da za su yi amfani da wannan kyautar wajen aikata abubuwan da suka dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel