Shugaban Bankin Access, Herbert Wigwe, matarsa da 'dansa sunyi hatsari a jirgi mai saukan ungulu

Shugaban Bankin Access, Herbert Wigwe, matarsa da 'dansa sunyi hatsari a jirgi mai saukan ungulu

  • Wata jirgin sama mai saukan ungulu dauke da Herbert Wigwe da wasu mutane 5 ta yi hatsari a daren Juma'a a yankiin San Bernardino
  • Wigwe, daya cikin wadanda suka kafa Bankin Access, yana tare da matarsa, dansa da kuma Abimbola Ogunbanjo, tsohon shugaban NGX
  • Rahotanni sun yi ikirarin cewa babu wanda ya yi rai a jirgin zuwa safiyar ranar Asabar, yayin da ake cigaba da aikin ceto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Rahotanni da suka fito sun nuna cewa shugaban kamfanin Access Holdings, Herbert Wigwe ya yi hatsari a cikin jirgi mai saukan ungulu yayin da ya ke Amurka a ranar Juma'a.

Herbert Wigwe ya mutu a Amurka
Shugaban Access Holdings, Herbert Wige, matarsa da 'dansa sunyi hatsarin jirgin sama a Amurka. Hoto: @HerbertOWigwe
Asali: Twitter

A cewar rahotanni daban-daban, ciki har da The Cable, lamarin ya faru a California kusa da iyakar Nevada, inda Wigwe, ke tare da matarsa da dansa.

Kara karanta wannan

Okonjo-Iweala, Atiku sun yi martani bayan an tabbatar da mutuwar Herbert Wigwe, matarsa da dansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin mai saukan ungulu na dauke da fasinjoji shida, cikinsu har da Abimbola Ogunbanjo, shugaban Kamfanin Nigerian Exchange Group Plc.

Kawo yanzu bankin na Access bai riga ya fitar da sanarwa ba dangane da afkuwar lamarin.

Yadda jirgin da ke dauke da Wigwe

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama na Amurka ta ce jirgin Eurocopter EC130 ya yi hatsari ne misalin karfe 10 na dare kusa da Nipton, California.

A cewar Premium Times, lamarin mara dadi ya ritsa da N130CZ, wacce kamfanin Orbic Air LLC, ke kula da shi ya baro Palm Springs, California misalin karfe 8.45 na dare.

Sai dai, a karshe an gano yana kusa da Fort/Barstow, misalin karfe 9.49 na daren ranar Juma'a.

An sanar da 'yan sandan San Bernardino game da hatsarin jirgin misalin karfe 10.12 na dare.

Mara Rodriguez, jami'in watsa labarai na 'yan sandan, ya ce hatsarin ya faru kusa da Halloran Springs Road.

Kara karanta wannan

"Rayuwa babbar kyauta ce": Sakon karshe da shugaban bankin Access ya saki kafin hatsarin jirgi

Legit Hausa ba za ta iya tabbatarwa idan akwai wadanda suka yi rai ba amma mutane sun fara martani kan lamarin a sashin sada zumunta.

A lokacin hada wannan rahoton, Bankin Access ba riga ya ce komai ba kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel