Herbert Wigwe: Abubuwan Sani 8 Game da Shugaban Bankin Access da Ya Mutu a Hatsarin Jirgi

Herbert Wigwe: Abubuwan Sani 8 Game da Shugaban Bankin Access da Ya Mutu a Hatsarin Jirgi

 • An yi babban rashi a Najeriya na shugaban kamfanin Access Holdings, Herbert Wigwe wanda ya rasu a ranar Juma'a, 9 ga watan Fabrairu
 • Herbert Wigwe ya rasu ne a wani hatsarin jirgin sama tare da matarsa da ɗansa tare da wasu fasinjoji da ke cikin jirgin
 • Marigayin sananne a ɓangaren harkokin banki a Najeriya da nahiyar Afirika, inda ya samu kyaututtuka masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

California, Amurka - Shugaban kamfanin Access Holdings, Herbert Wigwe, ya rigamu gidan gaskiya.

Shugaban bankin na Access ya rasu ne bayan jirgi mai saukar angulu da ke ɗauke da shi da wasu fasinjoji guda biyar ya yi hatsari a birnin California na ƙasar Amurka.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Herbert Wigwe ya rasu
Abubuwan sani dangane da rayuwar marigayi Herbert Wigwe Hoto: @HerbertOWigwe
Asali: Twitter

Ƴan Najeriya dai na ci gaba da jimamin rashin ɗaya daga cikin manyan masana harkokin banki a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani a kan Herbert Wigwe

Jaridar Daily Trust ta tattaro wasu abubuwan da ya kamata ku sani kan marigayi Herbert Wigwe.

Ga su a ƙasa kamar haka:

 • An haifi Herbert Wigwe a Ibadan, jihar Oyo a ranar, 15 ga watan Agustan 1966, wanda hakan ya sanya yake da shekara 58.
 • Ya samu digirinsa na farko a fannin Accountancy daga jami'ar 'University of Nigeria', da ke Nsukka, a jihar Enugu.
 • Wigwe ya fara aiki a kamfanin Coopers & Lybrand, da ke Legas.
 • Ƙwararren masanin kan harkokin bankin yana da kwalin MA a fannin 'Banking and Finance' daga jami'ar 'University College of North Wales (wacce yanzu ake kira da Bangor), da digirin digirgir a fannin 'Financial Economics' daga jami'ar Landan.
 • Wigwe shi ne babban manaja/shugaba na bankin Access daga watan Janairun 2014 zuwa watan Afrilun 2022.
 • Jaridun Vanguard da The Sun sun ba Wigwe kyautar masanin harkokin banki na shekara a shekarar 2016.
 • An kuma ba shi kyautar masanin harkokin banki na nahiyar Afirika na shekarar 2021, a wajen ba da kyaututtukan masana harkokin banki na nahiyar Afirika a shekarar 2021.
 • Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba Wigwe kyautar girmamawa ta ƙasa ta 'Commander of the Order of the Niger' (CON) a watan Oktoban 2022.

Kara karanta wannan

AFCON: Fitaccen ɗan kasuwa ya mutu yana tsaka da kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu

Hadimin Zulum Ya Rasu a India

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai magana da yawun gwamnan jihar Borno, Farfesa Umara Zulum, Isah Gusau ya rigamu gidan gaskiya.

Isah Gusau ya rasu ne a ƙasar India inda yaje jinyar wata cuta da take damunsa wacce ba a bayyana kowace iri ba ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel