Majalisa Ta Yi Magana Kan Matan da Aka Sace a Borno, Ta Tabo Jami'an Tsaro

Majalisa Ta Yi Magana Kan Matan da Aka Sace a Borno, Ta Tabo Jami'an Tsaro

  • Ƴan majalisar wakilai sun nuna takaicinsu kan yin garkuwa da mata sama da 300 da ƴan ta'addan Boko Haram suka yi a jihar Borno
  • Zainab Gimba ta gabatar da ƙuduri mai muhimmanci a gaban majalisar kan sace matan da aka yi a mazaɓar da ta ke wakilta
  • Ta buƙaci jami'an tsaro su gaggauta kuɓutar da matan daga hannun tsageru waɗanda aka sace bayan sun shiga daji neman itace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƴan majalisar wakilai sun buƙaci hukumomin tsaro da su kubutar da mata kimanin 300 da aka yi garkuwa da su a jihar Borno a makon jiya.

An bayyana cewa wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka yi garkuwa da matan a lokacin da suke neman itace a dajin Gamborou Ngala.

Kara karanta wannan

Majalisa ta buƙaci Shugaba Tinubu ya gaggauta kawo ƙarshen ƴan bindiga a Jihar Arewa

'Yan majalisa sun magantu kan sace mata a Borno
'Yan majalisa sun bukaci a ceto matan da aka sace a Borno Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce da take gabatar da ƙudiri kan lamarin a zauren majalisar a ranar Alhamis, ƴar majalisa mai wakiltar mazabar Bama/Ngala/Kalabalge ta jihar Borno, Zainab Gimba, ta bayyana sace ƴan matan a matsayin abin damuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan majalisa sun damu da sace mata a Borno

Ta ce sace matan abin sosa zuciya ne kamar yadda aka sace ƴan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok a watan Afrilun 2014, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.

A kalamanta:

"Ina so in sanar da majalisar cewa an sace mata kimanin 300 a lokacin da suke nemo itacen amfani a gida da sayarwa a mazaɓa ta.
"Ina kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ganin an ceto waɗannan matan da suka je neman abincinsu na yau da kullum.
"Majalisar ta lura cewa wannan shi ne sace-sace mafi girma karo na biyu bayan sace ƴan matan Chibok da aka yi a shekarar 2014 duk da cewa, har yanzu wasu daga cikin waɗannan ƴan matan na hannunsu."

Kara karanta wannan

Shugabannin majalisa za su gana da Shugaba Tinubu, bayanai sun fito

A nasa jawabin mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara kaimi wajen ceto matan da aka sace.

Bayan da majalisar ta amince da ƙudurin, an miƙa shi ga kwamitin tsaro da hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa.

Majalisa ta fara binciken NPC

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta umurci kwamitinta kan ƙidayar jama'a da ya gudanar da bincike kan yadda aka kashe N200b a shirin kidayar shekarar 2023 a lokacin gwamnatin Buhari

Majalisar ta umurci kwamitin da ya gayyaci babban daraktan hukumar kula da kidayar jama’a ta kasa (NPC) domin ya bayar da bayanin yadda aka kashe kuɗaɗen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel