Tsadar Rayuwa: Hotuna Sun Bayyana Yayin da Aka Gudanar da Salloli Na Musamman a Zaria

Tsadar Rayuwa: Hotuna Sun Bayyana Yayin da Aka Gudanar da Salloli Na Musamman a Zaria

  • Ƴan Najeriya sun fara gudanar da salloli a a kan halin da tattalin arziƙin ƙasar nan ke ciki wanda ya jefa mutane da dama cikin yunwa
  • Ɗaruruwan al’ummar Musulmi maza da mata ne suka yi dandazo a garin Zaria na jihar Kaduna domin gudanar da salloli
  • Suleiman Ibrahim, shugaban ƙungiyar makarantun Islamiyya a Zaria, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su haɗa kai a wannan mawuyacin lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Zaria, jihar Kaduna - Al’ummar musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun haɗu domin gudanar da salloli na musamman, inda suka nemi Allah ya kawo mana sauƙin matsalolin da ƴan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Wannan sallah ta musamman ta gudana ne a filin sallar idi na Mallawa, inda ta samu halartar maza da mata daga sassa daban-daban na garin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ministan Tinubu ya fadi dalili 1 da ya sa mutanen yankinsa ba za su yi zanga-zanga ba

An gudanar da salloli a Zaria
'Yan Najeriya na cikin halin kunci kan tsadar rayuwa Hoto: trustradio.com
Asali: UGC

Yadda aka yi sallah ta muamman a Zariya

Malam Muhammadu Sani Labudda, babban limamin masallacin Juma’a na Bakin Kasuwa (Tudun Wada) ne ya jagoranci sallar, inda ya bayyana cewa wahalhalun da ake fama da su sun yi tsanani, ya kuma yi kira da a kawo ɗauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa al’amuran da ke faruwa a ƙasar nan sun yi muni matuƙa, wanda hakan ke buƙatar yin addu’o’i tare, musamman yadda farashin kayayyakin masarufi ke ci gaba da hauhawa a kullum, a daidai lokacin da watan Ramadan ke gabatowa.

Malaman addini sun yi kira da a haɗa kai a Najeriya

Bayan kammala sallar, shugaban ƙungiyar makarantun Islamiyya ta Zaria, Suleiman Ibrahim, ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa:

"Wannan lokaci ne da ya kamata mutane su taru don ƙarfafa imaninsu da inganta ibadarsu domin Allah ya kawo taimako ga jama'a."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP zai ba 'yan adawa mukamai masu gwabi a jiharsa, ya fadi dalili

Suleiman ya buƙaci musulmai da su ba da fifiko wajen taimakon masu ƙaramin ƙarfi da nisantar ɗabi’un saɓo don neman tuba, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Sheikh Muhammadu Dan Tine Habibi da Umar Dikko Mai Shinkafa sun jaddada muhimmancin yin addu'o'i na musamman a lokutan da mutane ke fuskantar ƙalubale.

Sun shawarci al’ummar musulmi da su ci gaba da tsoron Allah da neman gafarar laifuffukan da suka yi don neman taimakon ubangiji.

Mazauna Abuja Sun Haƙura da Cin Nama

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mazaunan babban birnin tarayya Abuja, sun haƙura da cin nama saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita.

Mutanen sun rungumi Awara a madadin nama tun bayan da naman ya yi tsadar da sai wane da wane ka iya cire kuɗi su siya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel