Innalillahi: Tagwayen Bam Sun Hallaka Mutum 2 Tare da Raunata 6 a Borno, Bayanai Sun Fito

Innalillahi: Tagwayen Bam Sun Hallaka Mutum 2 Tare da Raunata 6 a Borno, Bayanai Sun Fito

  • Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu bayan wasu tagwayen bam sun fashe inda mutane shida suka samu munanan raunuka
  • Bama-baman sun fashe ne a wasu ma’aikatu biyu daban-daban a karamar hukumar Dikwa da ke jihar Borno a Arewa maso gabas
  • Bam din na farko ya yi ajalin wani lebura da ya dako bulolluka don aikin gini a makaranar Koibe yayin da na biyu ya yi ajalin wani a bayan gari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno – Wasu leburori biyu sun rasa ransu bayan bam guda biyu sun tarwatse a wurin aiki da ke karamar Dikwa a jihar Borno.

Rahotanni sun tabbatar da cewa bam na farko ya fashe ne a makarantar firamare ta Koibe da ke jihar, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi alawus, bayanai sun fito

Tagwayen bam sun fashe tare da hallaka mutane 2 da raunata wasu 6
Harin ya yi ajalin mutane biyu da raunata mutum shida. Hoto; Babagana Zulum.
Asali: Facebook

Mutane nawa suka mutu a fashewar bam din?

Bam din ya fashe lokacin da wani labura ya dauko bulolluka zuwa wani bangare na makarantar ashe bai san ya na dauke da bam din ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce bam na biyu kuwa ya fashe inda ya hallaka wani lebura a bayan garin Koibe da ke jihar.

ZagazolaMakama ta tabbatar da cewa bayan mutuwar mutanen biyu, akalla mutane shida ne suka samu munanan raunuka.

A watan Janarun wannan shekara, bam ya tarwatse da wasu yaran Islamiyya a karamar hukumar Gubio da ke jihar.

Matakin da Zulum ya dauka kan 'yan bola jari

Akalla yara guda shida ne suka mutu yayin tarwatsewar bam din wanda aka yi tsammanin kayan karfunan bola jari ne.

A shekarar 2023 ce Gwamna Babagana Zulum ya dakatar da dukkan ayyukan ‘yan bola jari a dukkan kananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

Babban labari: Tinubu ya shirya amfani da rahoton Oronsaye, zai yi wani babban sauyi a Najeriya

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne ganin yadda ayyukan nasu ke jawo matsaloli da rasa rayuka a jihar.

Zulum ya kori shugaban sansanin gudun hijira

Kun ji cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya fatattaki wani shugaban sandanin ‘yan gudun hijira da ke Bama.

Gwamna Zulum ya dauki wannan matakin ne kan zargin salwantar da kayan sansanin da shugaban ke yi lokuta da dama.

Shugaban sansanin wanda kuma ya ke jagorantar hukumar ba da agaji ta SEMA ana zarginsa da sace kayan sansanin tare da siyar da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel