'Yan Bindiga 2 Sun Saduda Yayin da Suka Mika Wuya Ga 'Yan Banga a Arewa, Sun Fadi Dalili

'Yan Bindiga 2 Sun Saduda Yayin da Suka Mika Wuya Ga 'Yan Banga a Arewa, Sun Fadi Dalili

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga biyu sun saduda tare da mika wuya ga kungiyar maharba a jihar Taraba
  • 'Yan bindigar, Gayya Alhaji Abdu da Siyyo Alhaji Amadu, sun nuna sha'awarsu na son bayar da gudunmawa wajen yaki da miyagu a jihar
  • Shugaban kungiyar maharba a jihar, Babangida Kwamando, ya ce suna karbar tubabbun masu aikata laifi bayan sun sa su rantsuwa da Qur'ani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Taraba - Wasu kasurguman masu garkuwa da mutane biyu, Gayya Alhaji Abdu mai shekaru 20 da Siyyo Alhaji Amadu mai shekaru 21, sun tuba sannan suka mika kansu ga shugaban maharba a jihar Taraba.

'Yan bindigar sun bayyana cewa su da kansu suka yanke shawarar daina yin wannan harka ta garkuwa da bayin Allah.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tagwayen bam sun hallaka mutum 2 tare da raunata 6 a Borno, bayanai sun fito

Wasu 'yan bindiga 2 sun mika wuya a jihar Taraba
'Yan Bindiga 2 Sun Saduda Yayin da Suka Mika Wuya Ga 'Yan Banga a Arewa, Sun Fadi Dalili Hoto: @GovAgbuKefas
Asali: Twitter

Gayya ya bayyana cewa sau biyu yana garkuwa da mutane, kuma cewa a duk ayyukan da suka yi ya samu N200,000 bayan an biya naira miliyan 5 fansar kowani mutum da suka sace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da yasa na fara garkuwa da mutane, Gayya

Matashin ya ce ya shiga kungiyar masu garkuwa da mutane ne lokacin da ya samu labarin cewa yana cikin jerin mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutane.

Ya ce a lokacin da aka sanya sunansa cikin jerin wadanda ake nema, bai taba aikata kowani laifi ba balle a kai ga garkuwa da mutane, don haka ya tsere daga gidan mahaifinsa saboda yana ganin kashe shi za a yi da zaran an kama shi.

Gayya ya ci gaba da bayyana cewa ya tsere zuwa wajen wani abokinsa wanda ke yi wa masu garkuwa da mutane aiki a tsaunukan Jalingo, Kona da Lankabiri.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi alawus, bayanai sun fito

Ya ce:

"Abokina ne ya kai ne sansanin masu garkuwa da mutane a wani tsauni a yankin Kona. Kungiyar na karkashin ikon wani kasurgumin 'dan bindiga mai suna Bashe.
"A kan tsaunin, na ga mutane da dama da aka yi garkuwa da su saboda duk wanda aka sace sai a kai shi can sannan a sake shi bayan an biya kudin fansa.
"Na mika wuya ne saboda ba zan iya jure yanayin yadda ake yi wa mutanen da aka sace ba, bana so a kashe ni saboda jami'an tsaro ko maharba suna kashe yawancin masu garkuwa da mutane."

Ya kara da cewar yana so ya kasance cikin maharba da kuma bayar da gudunmawa wajen yaki da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.

Na sha yin garkuwa da mutane amma na shiryu, Ahmadu

A nashi bangaren, Ahmadu ya ce ya shiga kungiyar masu garkuwa da muta ne ne da kansa a yankin Mayo-Renewo da ke karamar hukumar Ardo-Kola.

Kara karanta wannan

Bayan jami'an sun kashe shugabannin 'yan bindiga, tsageru sun afkawa mutane a Kaduna

Ya sanar da manema labarai cewa ya bayar da gudunmawa a garkuwa da mutane sau da dama, amma sai ya yanke shawarar dainawa tare da tuba.

Ahmadu ya ce:

"Na yanke shawarar daina garkuwa da mutane da tuba saboda na gano cewa mugunta ne sace mutum 'dan uwana sannan na tilasta masa biyan kudin fansa."

Muna sa tubabbun 'yan ta'adda rantsuwa da Qur'ani, Kungiyar maharba

Da yake martani, Babangida Kwamando, shugaban maharban, ya ce a kullun yana karbar 'yan bindiga ko masu garkuwa da mutanen da suka mika wuya gare shi.

Ya ce kungiyar maharba tana karfafawa 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane gwiwar tuba, da daina aikata laifin da suke yi, rahoton BNN.

Ya ci gaba da cewa:

"Ana sa masu garkuwa da mutanen da 'yan bindiga yin rantsuwa da Qur'ani cewa ba za su sake aikata irin wannan laifi ba kafin a karbe su cikin kungiyar maharba."

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kai samame kan ƴan bindiga, sun samu gagarumar galaba a jihar Arewa

Sojoji sun gano rijiyoyin mai 40

A wani labari na daban, mun ji cewa dakarun sojojin kasa da ke Fatakwal har wa yau sun gano wasu rijiyoyi danyen mai sama da 40 da ba a san da su ba.

Rahoton da aka samu a This Day ya ce an gano wadannan rijiyoyi ne a kauyen Rumuekpe a karamar hukumar Emohua a Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng